Nigeria da Burtaniya za su yi hadaka wajen yaki da cin hanci da rashawa a cikin kasar

Nigeria da Burtaniya za su yi hadaka wajen yaki da cin hanci da rashawa a cikin kasar

- Gwamnatin kasar Burtaniya ta ce tana aiki kafada da kafada da Nigeria don yaki da cin hanci da rashawa

- Wakiliyar Burtaniya, Ambasada Karen Pierce ta ce kasashen biyu zasu yi aiki tare don wayarwa al’uma kai dangane da illolin rashawa

-A cewarta, wannan hadakar zata sa duniya ta gane cewa Burtaniya ba mabuyar barayin gwamnati bane

Gwamnatin kasar Burtaniya ta ce tana aiki kafada da kafada da Nigeria don yaki da cin hanci da rashawa, ta hanyar samar da kayayyakin aiki na zamani ga manyan hukumomin da ke yaki da rashawa da yiwa dukiyar al’uma zagon kasa.

Babbar wakiliyar kasar Burtaniya a Majalisar Dinkin Duniya, Ambasada Karen Pierce, a wani taro kan magance rikice rikicen da ke cikin cin hanci da rashawa, tace kasashen biyu zasu yi aiki tare don wayarwa al’uma kai dangane da illolin rashawa.

Ta ce kasar Burtaniya na matukar tallafawa Majalisar Dinkin Duniya wajen yaki da cin hanci da rashawa, tana mai cewa ta gudanar da wani taro kan yaki da cin hanci da rashawa a kasar Landan, da nufin kawo karshen mummunar dabi’ar a kasashen duniya baki daya.

KARANTA WANNAN: Kwamishina yayi murabus don tsayawa takarar gwamnan jihar Ogun

Pierce ta ce: “Kwato kayayyakin gwamnati na daga cikin muhimman matakan dakile rashawa. A shekarun baya , mun gudanar da taro a karon farko kan hanyoyin da za’abi wajen kwato kayayyakin gwamnati a kasar Amurka, tare da hadin guiwa Babban Bankin Duniya da kuma ofishin dakile shan muggan kwayoyi da ta’addanci na majalisar dinkin duniya UNODC."

Nigeria da Burtaniya za su yi hadaka wajen yaki da cin hanci da rashawa a cikin kasar
Nigeria da Burtaniya za su yi hadaka wajen yaki da cin hanci da rashawa a cikin kasar
Asali: Twitter

Ta ce: “Burtaniya na son ganin ta yi aiki da kasashe don ganin an samar da ci gaba mai dorewa. A kasar Nigeria, mun samar da gudunmowar kayyakin aiki na zamani ga wasu manyan hukumomin da ke yaki da cin hanci da rashawa, kuma muna kan aiki don wayarwa al’umma kai akan Rashawa.”

Wakiliyar kasar ta Burtaniya ta yi nuni da cewa babu wata kasa da ke da rigakafin cin hanci da rashawa, tana mai cewa ana rasa Biliyoyin daloli ga cin hanci da rashawa a kowace shekara.

Ta kuma alakanta cin hanci da rashawa da ta’addandci a matsayin annobar da ke zuwa a lokaci daya, wadanda ke haddasa mafi yawan rikice rikicen da ake yi a duniya.

A cewarta, wannan hadakar tsakanin Burtaniya da Nigeria, zai sa duniya ta gane cewa Burtaniya ba mabuyar barayin gwamnati bane, ko yan kasuwa da jami’ai da ke satar kudade suna kaiwa ajiya kasashen waje.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel