Saraki, Atiku, Kwankwaso sun ja daga kan tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP
Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, jigan-jigan 'yan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, sun haye kan Kujerar naƙi kan amincewa da yarjejeniyar tsayar da dan takara guda da zai wakilci jam'iyyar a yayin zaben 2019.
Manema tikitin takara na jam'iyyar da kowanen su a halin yanzu ya ja daga ta hankoron kujerar shugaban kasa sun hadar da; shugaban majalisar dattawa; Abubakar Bukola Saraki, Tsohon gwamna kuma Sanatan Kano a tsakiya; Rabi'u Musa Kwankwaso da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa; Alhaji Atiku Abubakar.
A halin yanzu jam'iyyar ta PDP da sanadin jagoranci na wani jigo na ta, Walid Jibrin, ta kafa wani kwamiti domin tuntube-tuntunbe na kulla yarjejeniya tsakanin 'yan takara na jam'iyyar domin fitar da gwani daya tilo da zai fafata a babban zabe na 2019.
Sai dai a yayin tuntubar jiga-jigan uku a karo daban-daban, kowanen su ya ja daga tare da ikirarin dukkan wanda ya iya allon sa ya wanke domin tabbatar da shirin su kan zaben fidda gwani da jam'iyyar za ta gudanar bisa tsari da kuma tafarki na dimokuradiyyar kasar nan.
A yayin bayyana jajircewarsa da nuna rashin janye jiki, shugaban majalisar dattawa ya bayyana cewa, wannan karo ya kamata Najeriya ta fitar da shugaban kasa daga yankin Arewa ta Tsakiya kasancewarsa haifaffen jihar Kwara.
Saraki yayi wannan furuci ne yayin ganawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa cikin Birnin Makurdi na jihar Benuwe yayin wani shawagi da yawon neman goyan bayan da kuma ci gaba da jajircewa kan yakin neman zabe.
KARANTA KUMA: 'Yan Najeriya sun aminta da riƙon amanar mu - INEC ga PDP
Daga bangaren Turakin na Adamawa Alhaji Atiku Abubakar, Kakakin kwamitin yakin neman zaben sa, Mista Segun Sowunmi ya bayyana cewa, ya na da cikakken yakini Ubangidan sa ne zai lashe tikitin takara na jam'iyyar kuma bugu da kari ba bu wanda zai janyewa takarar sa a halin yanzu.
Kazalika tsohon gwamnan jihar Kano da sanadin Sakatariyar sa, Binta Spikin, ta bayyana cewa ba bu wani dan takara dake da cancanta gami da iko na lallasa shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019 face Ubangidanta Kwankwaso.
A yayin tuntubar kakakin tsohon gwamnan jihar Kaduna, wanda ya kasance daya daga cikin masu hankoron tikitin takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Sanata Ahmad Makarfi, ya bayyana cewa ba zai furta komai akan wannan lamari ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng