Matasa ne mafi yawan masu matsalar kwakwalwa a kasar nan - Bincike

Matasa ne mafi yawan masu matsalar kwakwalwa a kasar nan - Bincike

- Matasa ne kashi 85 cikin dari na mahaukata a Najeriya

- Kashi 40 cikin dari na matasan Najeriya na shaye shaye

- Kusan kwalabe miliyan 3 na maganin tari ake amfani dasu a kano a kowacce rana

Matasa ne mafi yawan masu matsalar kwakwalwa a kasar nan - Bincike
Matasa ne mafi yawan masu matsalar kwakwalwa a kasar nan - Bincike
Asali: Facebook

Dr Aliyu Abubakar, na asibitin koyarwa a jami'ar Ahmadu Bello, a Zaria, yace matasa ne kashi 85 na mahaukata dake Najeriya.

Abubakar ya fadi hakan ne a wani taron wayar da kai ga matasa da kungiyar cigaban matasa ta Bizara, a karamar hukumar Zaria, jihar Kaduna ta shirya.

Kamar yadda yace "matasa masu shekaru 18-38 ne suka kwashe kashi 85 na Mahaukatan da ke Najeriya. Manyan abubuwan da ke kawo hauka yanzu sun wuce kwayoyi. Matasa yanzu suna shakar kashin kadangare, kashin doki, da dai sauran su.

Yace a Najeriya an ruwaito cewa, kusan kwalaben maganin tari miliyan 3 ke karewa kullum a kano kuma kusan kwalabe miliyan 6 a arewa maso yamma.

Abubakar yace NDLEA ta ruwaito cewa kashi 40 cikin dari na matasan Najeriya suna shaye shaye.

DUBA WANNAN: Musayar kujera ta hada sanata fada da gwamna

Likitan ya jaddada cewa shaye shaye na kawo illoli kamar hauka, ciwon hanta, ciwon zuciya da sauran su.

Ya kara da cewa, masu shaye shaye na fadawa miyagun dabi'u irin su barin makaranta, kungiyar asiri, fashi da makami, kashe mutane da dai sauran dabi'u da suka sabawa al'adu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel