An rubutawa Shugaban kasa Buhari wasika game da shigowar Shekarau APC

An rubutawa Shugaban kasa Buhari wasika game da shigowar Shekarau APC

Mun samu labari cewa komawar tsohon Gwamna Malam Ibrahim Shekarau Jam’iyyar APC ke da wuya ta sa an fara korafi a Jihar. A makon da ya wuce ne Shekarau da Mabiyan sa su ka bar PDP.

An rubutawa Shugaban kasa Buhari wasika game da shigowar Shekarau APC
APC na kokarin ba Shekarau takarar kujerar Kwankwaso a 2019
Asali: Depositphotos

Wata Kungiya mai suna BUHARI 100 PER CENT ta aikawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari wasika inda ta koka da zaluncin da aka yi na mikawa tsohon Gwamnan Kano Ibrahim Shekarau kujerar Sanatan Jihar a APC a sama.

Kungiyar da ke da irin muradun Shugaba Buhari ba tayi na’am da tikitin da Jam’iyyar APC ke shirin ba tsohon Gwamna Shekarau a bagas ba daga shigowar sa Jam’iyyar a makon da ya gabata don haka ta nemi Buhari ya sa baki.

Ana rade-radin cewa Ibrahim Shekarau zai yi takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya a zaben 2019 wanda hakan ma yana cikin dalilan da su ka sa aka jawo tsohon Gwamnan da wasu dinbin Mabiyan sa cikin Jam’iyyar APC.

KU KARANTA: Sabon rikici ya kunno kai a Jam'iyar PDP

Kungiyar ta BUHARI 100 PER CENT ta nuna cewa Shekarau din ya sauya-sheka ne daga PDP zuwa APC ba wai don yana da ra’ayin Jam’iyyar APC ba sai dai kurum don san rai da cin ma burin siyasa bayan Jam'iyyar PDP ta gagare sa.

Har wa yau Magoya bayan Shugaba Buhari sun tuna masa lokacin da Shekarau ya rika kiran sa da sunaye iri-iri yana ci masa mutunci. Wannan Kungiya dai ta nemi a bada dama ayi zaben adalci wajen tsaida ‘Yan takaran APC a 2019.

A makon da ya wuce ne tsohon Gwamnan Kano Ibrahim Shekarau ya fice daga Jam’iyyar PDP ya dawo Jam’iyyar APC. Yanzu dai ana tunani an yi masa alkawarin kujerar da tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso yake kai a APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel