Shugaban kasa Buhari ya gana da Fastocin ‘Darikar Katolika

Shugaban kasa Buhari ya gana da Fastocin ‘Darikar Katolika

Labari ya zo mana cewa jiya Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gana da manyan Fastocin ‘Darikar Katolika na Mabiya addinin Kirista. An yi wannan babban taro ne a cikin Garin Sokoto.

Shugaban kasa Buhari ya gana da Fastocin ‘Darikar Katolika
Shugaban kasa Buhari yace bai da wata manufar Musulunci a Najeriya
Asali: Facebook

Shugaba Muhammadu Buhari ya fadawa shugabannin Kiristocin kasar cewa babu wani shiri da Gwamnatin sa ta ke yi na murkushe Kiristoci ko kuma musuluntar da Najeriya. Buhari yace farfaganda ce kurum jama’a ke yadawa maras tushe.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Shugaban kasar ya zargi wasu ‘Yan siyasa da yada irin wadannan karya domin batawa Gwamnatin sa suna da kuma kawo rikici tsakanin Kiristoci da sauran Jama’a alhali babu burbushin gaskiya a maganar.

Shugaba Buhari yayi wannan jawabi ne ta bakin Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha inda yace daga cikin zargin da ake yi masa shi ne jefa Najeriya cikin Kungiyar OIC ta Musulunci a baya sannan kuma da kokarin dabbaka shari’a.

KU KARANTA: Boko Haram sun sake kai sabon hari sansanin sojoji a Borno

Boss yace ana kuma zargin wannan Gwamnati da kokarin kafa munafar musulunci ta rikicin Makiyaya da Manoma da kuma ta’addancin Boko Haram. Shugaban kasar yace duk babu hannun sa a wannan rikici sai dai ana kokarin yi masa sharri.

Shugaban Kasar ya kara da cewa an kashe Musulmai da Kiristoci a wannan rikici da ake fama da su inda yake sa ran cewa an kusa ganin karshen su. Shugaban ya nemi Malaman addinin su wayar da kan Mabiyan su daga wannan mummunar farfaganda.

Wasu daga cikin manyan Fastocin sun yi magana wajen taron inda su ka nemi jama’a su yi zabi mai kyau a zaben 2019. Mai Girma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III yayi magana a wajen wannan taro inda shi kuma ya nemi a hada kai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel