PDP ta tsaida Matawallen-Maradun a matsayin dan takararta na gwamnan jihar Zamfara

PDP ta tsaida Matawallen-Maradun a matsayin dan takararta na gwamnan jihar Zamfara

- Jam'iyyar PDP ta zabi tsohon dan majalisar wakilai ta tarayya, Alhaji Bello Matawallem-Maradun a matsayin dan takarar gwamnan jihar Zamfara

- Rahotanni sun bayyana cewa masu ruwa da tsaki na jam'iyyar, sun lallami Sanata Sahabi Ya'u, akan ya janye kudirinsa don baiwa Matawallen-Maradun dama

- Matawallen-Maradun ya yi alkawarin kawo karshen ta'addancin da ake yi a jihar, idan har ya samu nasara a 2019

Jam'iyyar PDP ta zabi tsohon dan majalisar wakilai ta tarayya, Alhaji Bello Matawallem-Maradun a matsayin dan takarar gwamnan jihar Zamfara karkashin inuwar jam'iyyar, a zabe na 2019 da ke gabatowa.

Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito cewa dan takarar ya samu wannan nasara ne bayan da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar suka zauna suka tantance yan takarar gwamna a jam'iyyar, inda daga karshe suka tsayar da shi a matsayin dan takararsu.

Rahotanni sun bayyana cewa masu ruwa da tsaki na jam'iyyar, sun lallami Sanata Sahabi Ya'u, akan ya janye kudirinsa don baiwa Matawallen-Maradun dama, wanda kuma sukayi nasarar hakan.

Wani jigo a jam'iyyar, Janar Aliyu Gusau, wanda ya gabatar da tsayayyen dan takarar ga mambobin jam'iyyar, ya ce: "Mun ji dadi da ya kasance yan takara biyu ne suka nuna sha'awar tsayawa takarar gwamna a karkashin jam'iyyarmu, la'akari da jam'iyyar adawarmu da ke yan takara akalla 10, masu neman kujerar gwamnan jihar."

PDP ta tsaida Matawallen-Maradun a matsayin dan takararta na gwamnan jihar Zamfara
PDP ta tsaida Matawallen-Maradun a matsayin dan takararta na gwamnan jihar Zamfara
Asali: Twitter

KARANTA WANNAN: Ghana ta rufe shaguna sama da 40 mallakin yan Nigeria, tare da cafke mutane 100

Ya ce: "Sai dai, biyo bayan zama da yin nazari, da kuma tantancewa da masu da tsaki sukayi, mun cimma matsaya guda daya, cewar dan takara daya ne kawai zamu tsayar, ba sai mun yi zaben fitar da gwani ba."

Gusau wanda ya bayyana wannan mataki a matsayin wani abun ci gaba, da ke nuni da alamomin nasara na jam'iyyar a babban zaben 2019, ya kuma bukaci mambobin jam'iyyar da su hada kawunansu tare da yin aiki kafada da kafada don samun nasararsu baki daya.

A nashi jawabin, Sanata Sahabi Ya'u, ya ce ya janye ne biyo bayan tausasa zuciyar da masu fada aji da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar suka yi masa, bisa jagorancin Gusau.

"A matsayina na dan jam'iyya mai biyayya, a shirye nake na saurari bukatu da shawarwarin masu ruwa da tsaki na jam'iyyar, da kuma yin aiki tukuru don ci gaban jam'iyyar baki daya," a cewar sa.

Da ya ke jawabin godiya, dan takarar gwamnan jihar, karkashin PDP, Alhaji Bello Matawallen-Maradun, ya godewa Sanata Ya'u, masu ruwa da tsaki da kuma kafatanin 'yayan jam'iyyar PDP na jihar, bisa goyon bayansu, tare da yin alkawarin cire kitse daga wuta a zaben 2019

Matawallen-Maradun ya yi alkawarin kawo karshen ta'addancin da ake yi a jihar, idan har ya samu nasara a 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel