Tsohon Kocin Real Madrid Zidane ya gindayawa Man Utd sharudan karbar aikin Mourinho

Tsohon Kocin Real Madrid Zidane ya gindayawa Man Utd sharudan karbar aikin Mourinho

Tsohon Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya lissafowa Kungiyar Manchester United sharudan sa idan har ta so ya dawi horas da ‘Yan wasan ta inda ya kawo jerin ‘Yan wasan da yake so a saya masa.

Tsohon Kocin Real Madrid Zidane ya gindayawa Man Utd sharudan karbar aikin Mourinho
Man Utd na neman kawo Zidane ya a madadin Mourinho
Asali: Getty Images

Babban Kocin ‘Dan kasar Faransa Zidane ya fadawa Kungiyar Manchester United cewa sai an kashe masa makudan kudi har fam Miliyan 300 na Euro idan zai canji Jose Mourinho a Kulob din.

‘Yan wasan da Zidane yake so sun hada da:

1. Edison Cavani

Zidane zai so ya ga ‘Dan wasan gaba Edison Cavani a Kulob din kafin ya karbi aikin horas da United. Yanzu haka dai an fara tunani cewa Jose Mourimho ba zai kai labari ba a Kungiyar.

2. Toni Kroos

Haka kuma tsohon Kocin na Real Madrid zai nemi a sayo masa wani tsohon ‘Dan wasan tsakiyar sa Toni Kroos idan har ana so a gan sa a Manchester. A baya Manchester ta nemi Kroos.

KU KARANTA: Labarin wani Attajirin Najeriya da ke rayuwa a waje

3. Thiago Alcantra

Har wa yau, babban Kocin zai so Manchester ta sayo masa tsohon ‘Dan wasan Barcelona. Shi ma dai Alcantar ‘Dan wasan tsakiya ne da yake bugawa Bayern Munich da Sifen wasa.

4. James Rodriguez

Zinedine Zidane zai kuma so ya ga an ajiye masa James Rodeiguez a kulob din idan har da gaske ana neman ya canji Mourinho. Zidane ne dai ya ba Bayern Munich aron James lokacin yana Real.

A baya kun ji cewa Koci Zinedine Zidane za su hade da Cristiano Ronaldo a Juventus inda ya taba taka leda kafin zuwan sa Madrid. A kakar bana ne Cristiano Ronaldo ya koma Kungiyar Juventus da taka leda.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel