Mu hadu a gaban Alkali: Abba Kyari zai maka Jaridar Punch a gaban Kotu

Mu hadu a gaban Alkali: Abba Kyari zai maka Jaridar Punch a gaban Kotu

Mun samu labari cewa Abba Kyari zai maka gidan Jaridar Punch a gaban Kotu bisa sharri da yake zargin an yi masa tare da bata masa suna a wani labari da aka rika bugawa kwanan nan na cewa ya karbi cin hancin Miliyan 30 na wani kwangila.

Mu hadu a gaban Alkali: Abba Kyari zai maka Jaridar Punch a gaban Kotu
Malam Abba Kyari zai maka gidan Jaridar Punch a gaban Alkali
Asali: Depositphotos

Tun kwanaki ne ake zargin Shugaban Ma’aikatan na Fadar Shugaban kasa da karbar wasu makudan miliyoyin kudi da sunan kwangilar shigo da motoci a fadar Shugaban kasa. Ana zargin Kyari ya damfari wani ‘Dan uwan sa kusanMiliyan 30.

Fadar Shugaban kasa tayi maza ta karyata wannan zargi da yake yawo yanzu a gari inda tace sharri ake yi wa Abba Kyari. Garba Shehu wanda yake magana da yawun Shugaba Buhari ya bayyana cewa babu gaskiya kan zargin da ake yi wa Kyari.

KU KARANTA: Ana hurowa EFCC wuta ta binciki badakalar wani kamfanin Tinubu

Babban Hadimin Shugaban kasa Buhari watau Shehu ya bayyana cewa babu lokacin da aka bada wata kwangilar shigo da motoci kirar Hilux a fadar Shugaban kasa kamar yadda ake rayawa. Malam Shehu yace labarin karya ne kurum aka yi ta kitsawa.

Garba Shehu a wani jawabi da ya fitar a yanar gizo ya wanke Mataimakin na sa daga zargin da ake jifar sa da shi. Shehu ya kara da cewa Jaridar Punch sun san cewa babu gaskiya a zargin amma su ka buga wannan labari don haka za su shiga Kotu.

Kwanaki Shugaban EFCC Ibrahim Magu yayi kokarin kama Shugaban Ma'aikatan da ke Fadar Shugaban kasa watau Abba Kyari amma hakan bai yiwu ba bayan da tsohon Shugaban Hukumar DSS Lawal Daura ya sanar da shi game da shirin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel