Yadda Kwankwaso da Uche suka kore ni daga PDP - Malam Shekarau

Yadda Kwankwaso da Uche suka kore ni daga PDP - Malam Shekarau

- Secondus da Kwankwaso sun taka rawar gani wurin fita ta PDP

- PDP ta ba Kwankwaso wuka da nama akan shugabannin jam'iyyar na kano

- Ya canza sheka ne a ranar asabar, washegarin zuwan Oshiomhole da Ganduje gidan shi

Yadda Kwankwaso da Uche suka kore ni daga PDP - Malam Shekarau
Yadda Kwankwaso da Uche suka kore ni daga PDP - Malam Shekarau
Asali: Original

Malam Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar Kano, yace Uche Secondus, shugaban jam'iyyar PDP ta kasa da Rabiu Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano, sun taka rawar gani gurin fitar shi daga jam'iyyar adawa.

Shekarau ya koma APC ne a ranar Asabar, washegarin da Adams Oshiomhole, shugaban APC da Abdullahi Ganduje, gwamnan jihar kano, suka same shi a gidan shi.

Ya sanar da mabiyanshi cewa ya bar jam'iyyar adawa ne saboda shugabannin jam'iyyar sun ba Kwankwaso wuka da nama akan reshen jam'iyyar na jihar Kano bayan da ya dawo jam'iyyar a watan Yuli.

A cikin watan yuli ne wasu daga cikin yan jam'iyyar APC suka koma PDP, har da Kwankwaso. Hakan yasa aka ba Kwankwaso wasu damammaki kamar haka:

DUBA WANNAN: An roki 'yan PDP kar su tsere bayan firamare

Kashi 51 na cikin shugabancin jam'iyyar shi zai zaba. Sauran yan jam'iyyar su rike kashi 49.

Sannan duk wani Dan takarar majalisar jiha ko ta tarayya da yazo ta gurin shi yana da tikitin zaben 2019.

Rashin amicewa ta da hakan ne yasa na canza sheka, na gane cewa babu adalci. Inji Shekarau

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel