Asirin wani kamfanin tsohon Gwamnan Legas Tinubu ya fara tonuwa

Asirin wani kamfanin tsohon Gwamnan Legas Tinubu ya fara tonuwa

Wani babban Lauya Adetunji Adegboyega ESG ya bankado asirin kamfanin Alpha Beta wanda ake tunani yana samun daurin gindi daga Gwamnati na yin abin da ya ga dama ba tare da an iya komai ba.

Asirin wani kamfanin tsohon Gwamnan Legas Tinubu ya fara tonuwa
Ana zargin wani kamfanin Tinibu da kin biyan Gwamnati haraji
Asali: UGC

An fara zargin wani babban kamfani na ALPHABETA CONSULTING da kin biyan Gwamnati haraji na makudan kudi har sama da Biliyan 100. Ana kuma zargin cewa Asiwaju Bola Tinubu na APC ne mai wannan babban kamfani.

Sahara Reporters ta bayyana cewa ana zargin wannan kamfani da kin biyan haraji da kuma keta dokokin safarar kudi na kasa. Tuni dai wadansu manyan Lauyoyi su ka rubutawa EFCC takarda cewa ta tuhumi wannan kamfani.

KU KARANTA: Manyan Gwamnati sun halarci daurin auren 'Diyar Malami

Lauyoyin su na zargin tsohon Gwamnan Legas kuma Jigo a Jam’iyyar APC mai mulki Bola Tinubu ne yake da wannan kamfani ko kuma yake da mafi yawan hannun jarin da ke ciki don haka su ke keta dokokin kasa hankali kwance.

Wadannan Lauyoyi sun bayyana cewa idan ana neman wata hujja a shirye su ke da su mikawa Hukuma. An kafa wannan Kamfani ne a lokacin Babatude Fowler yana shugaban Hukumar da ke tarawa Gwamnatin Jihar Legas haraji.

Gwamnatin Shugaba Buhari dai ta dare mulki ne da muradun yaki da cin hanci da satar dukiyar al’umma. A baya kuwa an tursasawa Kamfanin su Atiku na Intel har ta kai ya shiga tsari nan na Gwamnati na asusun bai daya na TSA.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel