Arziki: Tarihin attajirin Najeriya da ke aika wanki da gugar kayansa kasar Ingila

Arziki: Tarihin attajirin Najeriya da ke aika wanki da gugar kayansa kasar Ingila

A yau Legit.ng ta tsunduma rumbun tarihi ne inda ta kawo muku tarihin wani attaijri, Candido Da Rocha, wanda mutane da yawa ke ganin shine miliniya na farko da ya yi suna sosai a Najeriya.

An haifi Da Rocha ne a 1860, mahaifinsa, Joao bawa ne a Brazil amma daga baya ya dawo Najeriya inda ya zama hamshakin dan kasuwa. Sunan mahaifiyarsa Esan Da Rocha.

Da Rocha ya yi karatu a CMS Grammar School da ke Legas tare da marigayi Herbert Macauley inda ya kasance shine shugaban dalibai na makaranta.

A wancan zamanin Da Rocha ya shimfida bututun ruwan famfo zuwa unguwani da ake bukatar ruwa a Legas kamar Yaba Ebute, Metta da Lagos Island. An ruwaito cewa gidansa na gida na farko da aka gina tuka-tuka a Legas har daga baya turawan mulkin mallaka suka fara biyansa domin ya samarwa jihar Legas ruwa.

DUBA WANNAN: Daya daga cikin masu son takarar shugaban kasa a PDP ya janye

Arziki: Tarihin attajirin Najeriya da ke aika wanki da gugar kayansa kasar Ingila
Arziki: Tarihin attajirin Najeriya da ke aika wanki da gugar kayansa kasar Ingila
Asali: Depositphotos

Ya samu arzikin sosai da sana'ar sayar da ruwa har ta kai ga gwamnatin jihar Legas ta karbe kwangilar samar da ruwan daga hannunsa. Baya ga sayar da ruwa, ya kasance yana bayar da bashi ga attajirai ciki har da JH Doherty da Sedu Williams wanda suka kafa Native Bank a Legas

Arziki: Tarihin attajirin Najeriya da ke aika wanki da gugar kayansa kasar Ingila
Arziki: Tarihin attajirin Najeriya da ke aika wanki da gugar kayansa kasar Ingila
Asali: Getty Images

.Da Rocha ya zama biloniya ne lokacin da ya fara sana'ar sayar da zinari. Wani baturen Ingila ne yake son komawa gida sai ya yiwa Da Rocha tallan dankararen zinari inda ya sayar masa kan kudi £6000.

Daga bisani, Da Rocha ya narkar da zinarin ya kuma fara sayarwa kananan dilalan zinari inda ya samu ribar 200%.

Duk da yake baiyi aure na coci ko kotu ba, Da Rocha yana da 'da guda da kuma yara mata hudu da matansa uku suka haifa masa.

A hirar da Punch tayi da jikansa mai suna Angelica Oyediran, ta ce: "Candido Da Rocha yana hulda da turan Ingila sosai kuma suna mutunta shi sosai. Lokacin yakin duniya na biyu, Da Rocha ya bawa Ingila daya daga cikin Otal dinsa (Bonanza Hotel) inda aka ajiye wasu daliban Najeriya.

"Da Rocha baya son siyasa amma yana taimakon jama'a sosai. Musu kudi a wannan zamanin basu wanke kayansu da kansu. Da Rochas da Johnsons da Dohertys da Oluwas duk Ingila suka aikewa da kayan wankinsu. Wasu daga cikinsu na da riguna 60, wanduna 60, gajerun wanduna 60 dai dai sauran tufafi."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel