Yadda zan kawo karshen rikicin makiyaya idan na zama shugaban kasa - Makarfi
- Daya daga cikin masu neman tikitin takarar shugabancin kasa a PDP, Sanata Makarfi ya ce akwai wadanda ke daukan nauyin kashe-kashe a Najeriya
- Makarfi ya ce zai kawo karshen kashe-kashen muddin aka zabe shi a matsayin shugaban kasa kamar yadda ya magance kashe-kashe a jihar Kaduna
- Makarfi ya ce zubar da jinin da ake a Najeriya tayi yawa, ya zama dole a kawo karshen lamarin
Tsohon shugaban riko na PDP, Sanata Ahmed Mohammed Makarfi, ya ce an gaza kawo karshen kashe-kashen da ke faruwa a wasu sassan Najeriya saboda akwai wadanda suka hada baki domin ingiza rikicin.
Sai dai ya yi alkawarin kawo karshen kashe-kashen muddin ya samu tikitin takarar PDP kuma aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.
Tsohon gwamnan na jihar Kaduna, ya yi wannan furucin ne a ranar Juma'a yayin da ya tafi mayar da fam din takarar shugabancin kasar sa a ofishin PDP da ke Abuja.
DUBA WANNAN: Kanin Dankwambo ya fasa komawa APC, ya bayar da dalili
Makarfi ya ce zai maimaita abinda ya yi lokacin da ya ke gwamna a Kaduna na kawo karshen kashe-kashe a jihar tsakanin kabilu da mabiya addinai daban-daban.
"Ba zai taba yiwuwa kashe-kashen nan su cigaba da faruwa ba face akwai hadin bakin wasu mutane a kasar. Masu makircin zasu iya kasancewa daga kowanne bangare na kasar amma babu yadda za'ayi abubuwa su cigaba da faruwa haka ba tare da hadin baki ba."
"Idan aka zabe ni a matsayin shugaban kasa, zanyi amfani da kwarewata domin kawo karshe kashe-kashen kamar yadda nayi lokacin ina gwamna a jihar Kaduna. Wannan ba shaci-fadi bane saboda na yi shi a aikace," inji Makarfi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng