Sojojin Najeriya sun tsare wani dan majalisa a kan rikicin jihar Filato

Sojojin Najeriya sun tsare wani dan majalisa a kan rikicin jihar Filato

- Rigingimu masu nasaba da addini da kabilanci na nema komawa sabbi a sassan jihar Filato a ‘yan kwanakin nan

- Gwamnatin tarayya ta kafa wata rundunar jami’an tsaro ta hadin gwuiwa (Oeration Safe Haven (OPSH)) domin tabbatar da zaman lafiya a jihar

- A jiya, juma’a, ne rundunar ta OPSH ta tsare mamba a majalisar dokokin jihar Filato, Honarabul Peter Gyendeng, bayan ya yi kokarin kubutar da wani matashi daga hannun sojoji

A jiya, Juma’a, ne rundunar dakarun soji dake aikin tabbatar da zaman lafiya a Filato karkashin atisayen “Operation Safe Haven” (OPSH) ta tsare mamba a majalisar dokokin jihar, Honarabul Peter Gyendeng, bisa zarginsa da hannu a rigingimun dake faruwa a yankin karamar hukumar da yake wakilta, Barkin Ladi.

Jaridar Daily Trust a rawaito cewar dakarun soji sun tsare Honarabul Gyendeng ne a shekwatar rundunar OPSH dake Jos da misalign karfe 1:00 na rana bayan ya yi yunkurin ceton wani matashi da rundunar ke tsare das hi tsawon wata biyu.

Sojojin Najeriya sun tsare wani dan majalisa a kan rikicin jihar Filato
Sojojin Najeriya
Asali: Facebook

Simon Gimba, direban dan majalisar, ya shaidawa Daily Trust cewar sun rabu da maigidan nasa ne a ranar ta Juma’a bayan ya sanar da shi cewar zai shelkwatar OPSH domin fitar da wani matashi da rundunar soji ke tsare da shi bisa zargin hannunsa a wani rikici da ya afku a jihar.

DUBA WANNAN: Filato ta sake kamawa da wuta: An kashe mutane 11 da raunata wasu 12

Gimba ya kara da cewa, “ina samun labarin abinda ya faru sai na garzaya shelkwatar OPSH amma wasu sojoji sun hanani ganinsa tare da fada min cewar zasu cigaba da tsare shi sai kwamandansu ya dawo.”

Sai dai da aka tuntubi Manjo Adam Umar, jami’in hulda da jama’a da yada labarai na rundunar OPSH, ya ce labarin tsare dan majalisar bai isa kan teburinsa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng