CBN ta fara cirar kudadenta daga bankunan da ta caza da fitar wa da MTN kudi waje

CBN ta fara cirar kudadenta daga bankunan da ta caza da fitar wa da MTN kudi waje

- An caji bankuna hudu biliyoyin nairori saboda taimakawa MTN kwashe kudadenta

- CBN ta fara zare kudaden da ta caje su daga asusunsu na bankin

- Stanbic ya rasa kusan biliyan biyu a yau

CBN ta fara cirar kudadenta daga bankunan da ta caza da fitar wa da MTN kudi waje
CBN ta fara cirar kudadenta daga bankunan da ta caza da fitar wa da MTN kudi waje
Asali: UGC

A kokarin iyar da nufinsa kan bankunan da suka karya dokar fitar da kudade kasashen waje ba bisa qa'ida ba, babban bankin Najeriya, CBN, ya zare naira biliyan kusan biyu daga asusun bankin Stanbic IBTC, tarar da aka laqaba masa a makon jiya.

Bankunan hudu dai, sun taimakawa kamfanin MTN ne kwasar kudadensa, kusan dala biliyan takwas daga Najeriya, da mayar dasu Afirka ta kudu.

Matakin ya razana bankuna dake ayyukan boye don kwarar tattalin arzikin Najeriya.

DUBA WANNAN: Ziyarar Kwankwso ga CAN

Sauran bankunan da aka caza, kuma ake sa ran CBN zata kwashi kudin nasu sun hada da Citibank, Standard Chartered Bank, da Diamond Bank.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel