Kannywood: An yi sulhu tsakanin Adam Zango da Ali Nuhu
- An dade ana cece-kuce tsakanin abokan sana'ar biyu
- Alamu na nuna kamar yanzu an shirya
- Adam Zango ne yayi mubayi'a ga 'Sarki'

Asali: Twitter
Adam Zango, na fina-finan Hausa, ya shirya da Ali Nuhu tsohon ogansa, wanda suka babe a 'yan kwanakin baya.
Shirin nasu na zuwa ne bayan da Aliyun ya ci kyautar Jarumai a taronsu na 'yan fim.
Adam Zangon, yayi jinjina ga ogan nasa, inda ya kira shi da Sarki, kuma Oga, ya kuma taya shi murnar lashe kyautar.
A shafinsa na Instagram, Adam Zango, ya wallafa hotonsa da Ali Nuhun inda ya durqusa gaba nai, ya kuma ce 'tuba nake sarki'.
DUBA WANNAN: An zargi Road Saety da tsafi
Su kuma mabiya sun dauki abin da shewa, inda suka ce ai dama sun san fadan na manyan biyu na wasa ne.
Ali Nuhu dai ya zuwa yanzu bai mayar da martani ba.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng