Kowa ya sani: Yan siyasa ne manya manyan makiyan Nigeria - Ango Abdullahi

Kowa ya sani: Yan siyasa ne manya manyan makiyan Nigeria - Ango Abdullahi

- Mai magana da yawun zauren dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi ya dora alhakin lalacewar kasar ga yan Siyasa, yan jaridu, fannin shari'a da kuma masu kada kuri'a.

- Ya ce suna da bayanai na yadda masu son zama gwamnoni ke kashe sama da Naira Biliyan daya wajen zabe, kuma babu wanda zai iya karyata hakan

- Ango ya kara da cewa Arewa na bukatar garambawul fiye da kowace shiyya ta kasar.

A ranar Alhamis, kakakin zauren dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi, ya ce babbar matsalar da ke fuskantar demokaradiyar Nigeria ba ta wuce yan Siyasa, yan jaridu, fannin shari'a da kuma masu kada kuri'a.

Abdullahi, wanda ya bayyana hakan a wani taron lakca ga yan jarida, karkashin daukar nauyin hukumar da ke kula da gidajen rediyo na kasa (FRCN), reshen kungiyar yan jarida ta kasa NUJ ta jihar Oyo, ya ce laifin komai zai koma kan shuwagabanni idan har kasar ta karkace.

Ya jaddada cewa mazan jiya irinsu, Chief Obafemi Awolowo, Nnamdi Azikiwe da Ahmadu Bello, sun yiwa kasar aiki da zuciya daya don ci gaban kasar baki daya duk da cewar sun fito daga shiyyoyi daban daban, kuma kowannensu na da irin nasa horon.

KARANTA WANNAN: Yan Nigeria sun koka kan yawaitar Lalatattun N100, sun roki Shugaban kasa da CBN da a bugo sabbi

Kowa ya sani: Yan siyasa ne manya manyan makiyan Nigeria - Ango Abdullahi
Kowa ya sani: Yan siyasa ne manya manyan makiyan Nigeria - Ango Abdullahi
Asali: Depositphotos

Farfesa Ango, ya jefa tambayar dalilin da ya sa yan siyasa ke batar da makudan kudade don fuskantar zaben 2019, inda ya bayyana cewa dan siyasa na kwarai ba ya bukatar kashe makudan kudade, illa ya nuna kyawawan ayyuka ko kudirorinsa ga masu kada kuri'a.

Ya ce: "Sahun farko na mutanen da suka lalata kasar nan sune yan siyasa. Na biyunsu sune yan jarida, yayin da fannin shari'a ya ke a sahu na uku. Masu kada kuri'a ne a sahun karshe. Akan hanyata daga Abeokuta a yau (Alhamis), na ci karo da allunan tallar yan siyasa babu adadi. Gaba dayansu sun fito takara a zaben 2019, sun gurbatar da hanyoyi da alluran tallata hajarsu.

"Me ya sa suke son zama gwamnoni ko sanatoci? Idan har kana son zama gwamnan Oyo, zai fi kyau ka shiga lungu da sako na garuruwan mutane ka sanar da su dalilin da zaisa su zabe ka. Allunan tallata ka ba zasu iya yin magana ba, babu abunda mutane zasu karu da su illa dai idan suna son kallon kyawawan hotunanka.

KARANTA WANNAN: 2019: Ararume, Izunaso sun sauya sheka daga APC zuwa APGA

"Idan har wani na son zama shugaban kasata, dole in damu da sanin dalilin da yasa ya ke son ya shugabanci kasar. Kudaden da aka sanya na siyen fom din tsayawa takara sunyi tsada, sai dai fa idan gidauniyar bada tallafi ce aka bude.

"Muna da bayanai na yadda masu son zama gwamnoni ke kashe sama da Naira Biliyan daya wajen zabe, babu wanda zai iya karyata hakan. Me yasa zaka kashe har sama da Biliyan daya kawai don kana son zama gwamna? Ya zamar mana wajibi mu ilimantar da jama'a dalilin da yasa yan siyasa ke son dafa madafun iko.

Abdullahi ya ce ya samu ganawa da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a daren ranar Laraba, gabanin nan ya gana da shuwagabannin yankin Afenifere. Ya ce yan Nigeria zasu amfana da irin kokarin tuntuba da ya ke yia fadin kasar a fuskantar zaben 2019 da ake yi. Ya ce Arewa na bukatar garambawul fiye da kowace shiyya ta kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel