Gwamnatin Najeriya za ta samar da megawatt 89.6 domin bunkasa lantarki a Jami’o’in Tarayya
A halin yanzu dai mun ji labarin yadda Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ke mulki a Najeriya ta ke cigaba da kokarin inganta lantarki a wasu Jami’o’ da asibitocin kasar nan.

Asali: Depositphotos
Gwamnatin Buhari ta kawo wani tsari na EEP mai suna Energizing Education Programme. An kafa wannan shiri ne domin samar da wuta ba kaukautawa a Jami’o’in Gwamnatin Tarayya 37 da ake da su da kuma manyan asibitocin kasar.
Shugaba Buhari zai yi hobbasa wajen ganin an samar da wutan lantarki a manyan Jami’o’in Gwamnatin Tarayya da ake da su a fadin Najeriya. Haka kuma za a inganta wutan a manyan asibitocin koyon aiki 7 da ake da su.
KU KARANTA: Yadda wata Kungiya ta sayawa Buhai fam din takaran 2019
A wannan shiri na Gwamnatin APC, za a samar da kusan megawatt 90 wanda za su taimaka wajen ganin an rage samun matsalar dauke wuta a Makarantun Jami’o’in Gwamnati da kuma asibitocin da ake kwarewa wajen aikin likita.
Wannan Gwamnati ta na kuma sa ran kammala wasu ayyukan wutan lantarki da ta sa a gaba a shekarar nan. Ana sa ran kammala aikin wuta na Afam da kuma wata tasha da ke Kudenda. Akwai kuma wasu ayyuka da za a gama a Katsina.
Bayan hakan dai kun ji cewa Gwamnatin Shugaba Buhari ta na gina gidaje a Jihohi 34 na Najeriya domin samawa Ma’aikatan Gwamnati saukin mallakar gidaje zama. Tuni dai an yi nisa a wannan aiki a Jihohi irin su Kano da sauran su.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng