2019: Manyan ‘yan siyasan Zamfara sun daura damarar zama Gwamna

2019: Manyan ‘yan siyasan Zamfara sun daura damarar zama Gwamna

Yanzu haka wasu manyan ‘yan siyasan da ake ji da su a Jihar Zamfara sun fara neman kujerar Gwamna Abdulaziz Yari wanda yake shirin barin gado bayan wa’adin sa ya kama hanyar karewa.

2019: Manyan ‘yan siyasan Zamfara sun daura damarar zama Gwamna
Wasu 'yan siyasa na kukan ana neman hana su takara a Zamfara
Asali: UGC

Kawo yanzu mutum 3 sun nuna sha’awar tsayawa takarar Gwamna a Jihar Zamfara karkashin Jam’iyyar APC. Wadannan ‘Yan siyasa sun hada da:

1. Mahmud Aliyu Shinkafi

Tsohon Gwamna Alhaji Mahmud Shinkafi yana cikin masu harin kujerar Gwamna Abdulaziz Yari wanda ya doke shi lokacin yana mulki a 2011. Shinkafi wanda ya koma APC daga baya yana ganin cewa ya fi sauran ‘Yan takarar sanin mulki.

KU KARANTA: APC ta yi wani babban taro daf da lokacin zaben Osun

2019: Manyan ‘yan siyasan Zamfara sun daura damarar zama Gwamna
Sanata Kabiru Marafa yana cikin masu neman Gwamna a Zamfara
Asali: Depositphotos

2. Kabiru Marafa

Sanatan Zamfara Kabiru Marafa bai taba boye sha’awar mulkin Jihar ba inda ya ke sukar Gwamna Yari wajen tabarbarewar sha’anin tsaro a Jihar. A dalilin haka, kusan dai yanzu haka Jam’iyyar APC mai mulki ta samu bangaren taware a Jihar.

3. Aminu Jaji

Hon. Aminu Jaji wanda ke wakiltar a Kaura-Namoda/Birnin-Magaji Majalisa yana cikin masu harin kujerar Gwamna a Zamfara. A makon jiya ne Jaji ya samu fam din takara inda yace an yi kokarin hana sa. Jaji yace zai gyara Jihar idan ya samu mulki

A can cikin kwanakin baya Gwamna Abdulaziz Yari ya taba bayyana cewa zunuban jama’a na cikin abin da ya jawo cutar sankarau da aka rasa gane kan ta bayan cutar ta zagaye Jihohin kasar nan. Wannan kalamai na Gwamna dai ba su yi wa jama’a dadin ji ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel