Jigo a jam’iyyar PDP ya gamu da ajalinsa a hannun yan bindiga a jihar Adamawa

Jigo a jam’iyyar PDP ya gamu da ajalinsa a hannun yan bindiga a jihar Adamawa

Wasu gungun yan bindiga sun kai hari a jihar Adamawa inda suka halaka shugaban jam’iyyar PDP a mazabar Bare na cikin karamar hukumar Numan, Charles Chrisantus, inji rahoton jaridar Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun kashe Charles ne a gaban matarsa Dorcas a ranar 29 ga watan Agustan shekarar 2018, sai dai an jiyo uwargida Dorcas tana zargin Yansanda da kokarin kashe maganar.

KU KARANTA: Mazauna birnin Abuja sun firgita yayin da aka yi girgizan kasa da daddare

Da take zantawa da manema labaru a ofishin Yansanda, Dorcas tace hukunta wadanda suka kashe mijinta ne kawai zai kawo mata kwanciyar hankali, “A gabana maharan yan Fulani suka caccaka ma mijina wuka a wuya da cikinsa har sai da ya mutu, sa’annan suka datse kansa, suka tafi dashi.” Inji ta.

Sai dai hukumar Yansandan jihar ta gayyaci Dorcas da wasu mata guda uku a matsayin shaidu zuwa ofishin Yansandan farin kaya don su bada jawabin abinda suka sani, suna ofishin ne dangin mijin suka sanar da Dorcas cewa an gano inda yan bindigan suka buya.

Yan uwan mijinnata sun gano yan bindigan a wani Asibiti suna samun kulawa, da wannan ne Dorcas ta bayyana ma Yansanda cewa zata iya gane wadanda suka kashe mijinta, do haka ta roki Yansanda su rakata inda yan bindigan suke.

Sai dai Dorcas tace babu abinda Yansanda suka yi tun bayan amsan jawabansu, don haka tace ta fahimci kamar Yansanda suna baiwa yan bindigan kariya ne. shima shugaban matasan PDP a mazabar Bare, Tekas Adiel yace da fari Yansanda sun ce yan bindigan dake kai musu hari sun gudu, amma sai ga shi a ranar Talata sun sake kai musu hari.

A nasa jawabin, Kaakakin rundunar Yansandan jahar, Musa Habibu ya tabbatar ma majiyarmu cewa sun kama wasu daga cikin wadanda ake zargi da kashe shugaban na PDP, inda ya kara da cewa suna nan suna gudanar da bincike.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel