Buhari ya ginawa Ma’aikata gidaje fiye da 4000 – Fadar Shugaban kasa

Buhari ya ginawa Ma’aikata gidaje fiye da 4000 – Fadar Shugaban kasa

Shugaba Buhari yana ginawa Ma’aikata gidaje fiye da 4000 a cikin fadin kasar nan kamar yadda mu ka samu labari daga wani babban Hadimin Shugaban kasar a kafofin sadarwa na zamani.

Buhari ya ginawa Ma’aikata gidaje fiye da 4000 – Fadar Shugaban kasa
Gwamnatin Shugaban kasa Buhari ta gina gidaje da-dama cikin shekara 3
Asali: UGC

Kwanan nan ne Tolu Ogunlesi yayi karin haske game da wasu ayyuka na Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari musamman wajen gina abubuwan more rayuwa.Daga ciki akwai gidaje da Gwamnatin Tarayya ke ginawa.

Mai ba Shugaban Kasar shawara yayi amfani da shafin sa na Tuwita inda ya bayyana cewa kawo yanzu Gwamnatin Najeriya ta gina gidaje fiye da 580 a Jihar Nasatawa. Yanzu haka kuma ana gina wasu gidajen a kusan duka Jihohi.

KU KARANTA: Wasu tsofaffin Sojojin Najeriya sun tonawa kan su asiri

Ogunlesi ya bayyana cewa Gwamnatin Buhari tayi nisa a wannan aikin a irin su Jihar Kaduna, Ogun, Kaduna, da kuma Delta. Hadimin Shugaban kasar yace ana sa rai kwanan nan za a soma wannan aiki a Legas, da kuma Jihar Akwa Ibom.

Mista Ogunlesi wanda yana cikin masu ba Shugaban kasa shawara ya kuma tabbatar da cewa za a gina irin wannan kananan gidaje a babban Birnin Tarayya Abuja. A Kano dai tuni har an yi nisa domin an gina gidaje fiye 750 inji Hadimin na Buhari.

Kafin yanzu dai babu irin wannan tsari na gidaje a Najeriya. Bayan wannan dai Gwamnatin Buhari ta na kokari inganta wutan lantarki a wasu manyan Makarantu da ake ji da su a kasar nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel