'Yan kungiyar asiri sunzo hannu, sun zayyana yadda suke aikinsu

'Yan kungiyar asiri sunzo hannu, sun zayyana yadda suke aikinsu

- Anyi caraf da mutane uku yan kungiyar asirin Black Axe Confraternity

- Sun matsawa Al'ummar Ijanikin, Iyano-ishashi da Ojo

- Sunyi ajalin rayuka sama da 11

'Yan kungiyar asiri sunzo hannu, sun zayyana yadda suke aikinsu
'Yan kungiyar asiri sunzo hannu, sun zayyana yadda suke aikinsu
Asali: Depositphotos

Jami'an Special Tactical Squad, sun cafke mutane uku yan kungiyar asirin Black Axe Confraternity a Legas sakamakon kashe mutane fiye da 11 da sukayi a shekaru biyu da suka gabata.

Wadanda ake zargi sun hada da Nasiru Bashiru, Kenneth Dike da Power Michael.

An kama su ne inda suka kashe wani mutum mai matsakaicin shekaru, mai suna Walter, a hanyar shiga wani sanannen otal a Iyano-ishashi a jihar, a ranar 21 ga watan yuli.

DUBA WANNAN: ISIL sun shigo Najeriya

Jami'an yan sandan sun kama su bayan karar da aka kai a rubuce zuwa ga sifeto Janar din yan sanda, Ibrahim Idris.

Bayan hakan ne sifeto Janar din ya tura jami'an, inda suka damko su daga maboyar su.

Da majiyar mu ta samu tattaunawa da wadanda ake zargin, sun bayyana cewa suna da hannu gurin kashe mutane 11 a Ajegunle, Magbon da Ijanikin a jihar Legas kuma da sa hannun su a kisan Walter.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng