Matashi ya ce ga garinku bayan dan uwansa ya daba masa wuka a wuya

Matashi ya ce ga garinku bayan dan uwansa ya daba masa wuka a wuya

- Kotu ta bayar da umurnin tsare wani matashi a kurkuku saboda zarginsa da kashe dan uwansa

- An gano cewa matashin ya daba wa dan wansa wuka a wuya ne yayin da wata sabani da shiga tsakaninsu

- Sai dai wanke ake tuhuma da aikata laifin kisan bai amsa laifin ba

Wata babban kotu da ke zamanta a Akure, Jihar Ondo ta bayar da umurnin tsare wani matashi mai suna Odunayo Ikudehinbu, saboda zarginsa da kashe 'dan uwansa mai suna Segun Ikudehinbu.

Lamarin ya afku ne a Igbokoda da ke karamar hukumar Ilaje na jihar Ondo kamar yadda Punch ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta gano cewa wanda ake zargin ya dabawa Segun wuka ne yayin da suke samu sabani. An garzaya da Segun zuwa asibiti amma daga bisani sai ya ce ga garinku.

Matashi ya ce ga garinku bayan dan uwansa ya daba masa wuka a wuya
Matashi ya ce ga garinku bayan dan uwansa ya daba masa wuka a wuya
Asali: Twitter

Odunayo ya cika tsere amma daga baya jami'an hukumar 'yan sanda sun damko shi, kuma aka gurfanar dashi gaban kuliya bisa laifin kisar gilla.

DUBA WANNAN: Wasu na hannun daman 'yan takaran shugabancin kasa 2 a PDP za su koma APC

Da farko an dakatar da shari'ar saboda rashin lawyer da zao kare wanda ake tuhuma amma daga baya wani Olugbenga Adedibu, ya bayyana domin kare shi.

Kara ta ce, "A ranar 3 ga watan Disamban 2017, misalin karfe 10 na dare a gidan Ayodele da ke College Road a Igboka, Kai, Odunayo Ikudehinbu, ka bugawa wani Segun Ikudehinbu fitila a kansa kuma daga baya ka caka masa wuka a wuya wanda hakan ya yi sanadiyar rasuwarsa."

Sai dai wanda ake tuhumar bai amsa laifin kisar ba.

Alkalin kotun, Justice Samuel Bola, ya dage cigaba da sauraron karar har sai ranar 2 ga watan Oktoban 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel