Matsalar Tsaro: An fille kan dansanda a Jos

Matsalar Tsaro: An fille kan dansanda a Jos

- Dama can ana samun matsalar tsaro a kasar nan

- Hawan mulkin PAC abin ya kazanta

- Jihar Pulato na gaba-gaba wajen wannan balaharar

Matsalar Tsaro: An fille kan dansanda a Jos
Matsalar Tsaro: An fille kan dansanda a Jos
Asali: Depositphotos

An tsinci qoqon kan wani dansandan kasar nan an wullar a arewacin birnin Jos, a kan titin Zaria, kamar yadda rahotanni ke nuna wa.

An tsinci gawar ranar asabar amma sai yau ne hukumar 'yansandan jihar ta tabbatar da aika-aikar.

Kakakin hukumar na jihar, Tyopev Terna ya tabbatar wa da manema labarai cewa gawar ta ma'aikacin dansandan ne dake Mobile Police dake Sector 1 a Operation Safe Heaven a jihar, wadanda su ke aikin tabbatar da zaman laiya a yankin..

DUBA WANNAN: Kudin da Najeriya ke asara daga man fetur

An dai tabbatar da gawar ta MOPOL sergeant Unana Ishaya ce, wanda ya fita tun 1 ga Satumba, don sayen tsire, amma har yanzu bai dawo ba.

An ajje gawar a Mutuware, an kuma bude bincike a kan yadda lamarin ya kai ga haka.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel