Y’aƴan kungiyar matsafa sun yanke kan wani dansandan MOPOL a Jos

Y’aƴan kungiyar matsafa sun yanke kan wani dansandan MOPOL a Jos

An cigaba da samun munanan rahotanni dake fitowa daga jahar Filato musamman a yan kwanakin nan inda rikici tsakanin makiyaya da manoman jahar ke kara ta’azzara, sai dai a wannan karo wani dansanda aka halaka a garin.

Jaridar daily trust ta ruwaito an gano gangan jiki wani jami’in dansandan MOPOL babu kai a garin Jos na jahar Filato wanda ake zargin wasu yayan wata kungiyar asiri ne suka kashe shi.

KU KARANTA: Kungiyar magoya bayan shugaba Buhari ta biya masa naira miliyan 45 kudin takara

Majiyar Legit.ng ta ruwaito an gano gangan jikin ne a bayan filin kwallon kafa na cikin gari akan titin Zaria, cikin karamar hukumar Jos ta Arewa a ranar Laraba 5 ga watan Satumba.

Sai dai rundunar Yansandan jahar ta bayyana sunan dansandan a matsayin Unana Ishaya, kuma yana aiki da shiyya na 56 dake aikin tabbatar da tsaro tare da zaman lafiya a garin Jos, da ma sauran yankunan jahar Filato.

Kaakakin Yansandan jahar, DSP Terner Tyopev ya bayyana cewa a ranar asabar din data gabata ne aka kashe dansanda Unana jim kadan bayan ya fita daga Ofis da nufin za shi ya sayo tsire, ya kara da cewa sub samu labari mutuwar Unana ne a lokacin da wani Soja, Kyaftin Joer Olaruwaju ya sanar dasu.

Kaakaki Terna yace “Sajan Unana ya fita Ofis a ranar 1 ga watan Satumba da nufin za shi sayan nama, amma bai dawo ba, a yanzu mun mika gawarsa zuwa dakin ajiyan gawarwaki dake asibitin kwararru na jahar Filato, mun kaddamar da bincike don gano wadanda suka aikata wannan aiki.” Inji shi.

Sai dai wani babban jami’I daga kungiyar kasuwar Farar gida, kusa da inda lamarin ya faru ya bayyana cewa yana gida aka kirashi yazo yaga abinda ke faruwa a kasuwar, yace kallo daya ya iya yi ma gawar saboda babu kyawun gani, amma yace wannan aikin matsafa ne dake yanki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel