Kuji yawan kudin dake zurarewa waje bayan an hako mai daga kasar nan

Kuji yawan kudin dake zurarewa waje bayan an hako mai daga kasar nan

- Kashi 95 cikin dari na kudin dake shigowa yana zuwa aljihun waje ne

- Yan kasar nan basa amfana da ko gurbin aiyukan

- Dole ne gwamnati tayi hobbasa, inji kungiyar ma'aikatan sufurin ruwa

Kuji yawan kudin dake zurarewa waje bayan an hako mai daga kasar nan
Kuji yawan kudin dake zurarewa waje bayan an hako mai daga kasar nan
Asali: UGC

Cibiyar kiyaye sufurin ruwa (NIMASA) ta nuna damuwarta akan yanda kasashen waje ke amfana da bangaren sufurin ruwa kusan kashi 95 cikin dari.

Darakta Janar na cibiyar, Dr. Peterside Dakuku, yace hakan a wani taron da sukayi mai taken :Local content Development in shipping, oil and gas logistics operations in Nigeria, wanda kungiyar Maritime Reporters ta hada.

Mataimakiyar daraktan, Mrs Hannah Akpan ce ta wakilce shi, inda tace, kashi 95 na kudin da ake samu a duk shekara na miliyan 150 yana tafiya ne ga kasashen waje.

DUBA WANNAN: Agajin kamfanin Maltina ga ilimki a Kano

Yace, a kiyasin ma'aikatar, a duk shekara ana samun cargo na ton miliyan 150 wanda yake kawo ribar dala biliyan 50.

Amma kashi 95 yana tafiya ne ga kasashen waje, baya da rashin samar da aikin yi ga yan kasar da hakan keyi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel