Ya hallaka kansa garin kokarin zulle wa jami'an tsaro ya tsunduma ruwa

Ya hallaka kansa garin kokarin zulle wa jami'an tsaro ya tsunduma ruwa

- Wani Dan fashi ya gwammace mutuwar shi, da kamun yan sanda

- Ya fada gadar ne tare da duk samun su na ranar

- Yan fashin sun kware a daukar mutane a mota, inda suke kwace musu kudade da wayoyi

Ya hallaka kansa garin kokarin zulle wa jami'an tsaro ya tsunduma ruwa
Ya hallaka kansa garin kokarin zulle wa jami'an tsaro ya tsunduma ruwa
Asali: Twitter

Wani Dan fashi, mai suna Junior ya fada gada ta uku dake babbar hanyar Oshodi a jihar Legas.

Kamar yanda abokan fashin nashi, Amos Williams, Paul Olise da John Akinyemi suka shaida cewa sunyi wa mutane 4 fashi, wadanda suka hau motar su a Ketu/Alepere zuwa Oshodi.

A maimakon su sauke su a Oshodi, sai suka ba motar su wuta zuwa Iyana Oworo, inda suka cigaba zuwa kan doguwar gadar, bayan da suka dinga turo fasinjojin kasa bayan sun kwace kudaden su da wayoyin su.

DUBA WANNAN: Siyasar 2019 ta dauki dumi

Semiu Oluwaseun shine fasinja na farko da suka turo kasa. Dan babur ya taimake shi suka bi motar bayan da ya fada mishi abinda ya faru. A hanyar ne suka tarar da jami'an RRS, inda suka sanar dasu abinda ke faruwa.

Babu bata lokaci suka bi yan fashin. A lokacin da suka gane ana binsu ne suka tsaya kowa yayi ta kanshi. Inda Junior ya fada ruwa da dukiyar su, bayan da ababen hawa har guda biyu suka bige shi.

A halin yanzu dai ana cigaba da bincike, inda za a gurfanar dasu gaban kuliya bayan an kammala binciken.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel