Taron Berlin: Har yanzu akwai ‘Yan Boko Haram a tafkin Chad – Inji Kamaru

Taron Berlin: Har yanzu akwai ‘Yan Boko Haram a tafkin Chad – Inji Kamaru

Rahotanni sun zo mana cewa har yanzu ‘yan ta’addan Boko Haram na cigaba da barna a cikin Yankin Chad. Wani Gwamna a Kasar Kamaru ne ya bayyana wannan a wajen wani babban taro shekaran jiya.

Taron Berlin: Har yanzu akwai ‘Yan Boko Haram a tafkin Chad – Inji Kamaru
Shugaban Sojin Kasa na Najeriya Janar Tukur Buratai
Asali: UGC

Gwamna Mijinyawa Bakary na Arewacin Jihar Kamaru ya bayyana cewa akwai sauran aiki wajen yaki da ‘Yan Boko Haram. Mijinyawa Bakary yace ana samun karuwar barna a kan iyakar Chad cikin ‘yan kwanakin nan.

Gwamnan da yake jawabi wajen babban taron da aka shirya a Duniya a Garin Berlin na Kasar Jamus yace akwai ‘Yan ta’addan Boko Haram makil a Yankin Chadi kuma kawo yanzu akwai ‘yan gudun Hijira a Yankin.

KU KARANTA: An ba Shugaban Sojin Kasa na Najeriya lambar yabo

Gwamna Bakary yake cewa sama da mutum 100, 000 daga Najeriya ke labe a irin su Kasar Kamaru. Gwamnan yace su na bukatar taimakon kasashen Duniya domin su cigaba da rike ‘Yan Najeriya da ke cikin kasar sa.

Shi ma dai Gwamna Muhammadu Bakabe na Kasar Jamhuriyyar Nijar yace akwai mutum sama da 118, 000 da ke bukatar agajin gaggawa a kasar sa. Akwai dai dinbin jama’a da Boko Haram su ka tarkata zuwa Garin Diffa a Nijar.

A wajen taron dai manyan Kasashe da Kungiyoyin Duniya sun yi alkawarin taimakawa Afrika. Kafin nan dai Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babu inda ‘Yan Boko Haram su ke da iko da shi yanzu a cikin Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel