Gwamnatin Shugaba Buhari ta fara rabawa ‘Yan Najeriya bashin N10000

Gwamnatin Shugaba Buhari ta fara rabawa ‘Yan Najeriya bashin N10000

Mun samu labari cewa Gwamnatin Najeriya ta fara rabawa ‘Yan kasuwa bashi domin su karfafa karfin jarin su. Yanzu haka an fara da Jihar Osun inda aka ba ‘Yan kasuwa da dama kudi.

Gwamnatin Shugaba Buhari ta fara rabawa ‘Yan Najeriya bashin N10000
Shirin Trader Moni na Gwamnatin Buhari ya fara aiki a Jihar Osun
Asali: UGC

Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kaddamar da shirin wannan Gwamnati na rabawa wasu ‘Yan kasuwa bashin karin jari har na N10000 domin su tada sana’ar su.

Gwamnatin APC ta kawo wani shiri da ake kira Trader Moni wanda za a ba kananan ‘Yan kasuwa bashin jari na N10000 har zuwa N50000 wanda za a maida a cikin watanni shida.

Wannan tsari da yake cikin shirin GEEP watau “Government Enterprise and Empowerment Programme” wanda zai karfafa kasuwancin masu karamin karfi a fadin Najeriya.

Yanzu haka har an fara rabawa wadannan kudi a Jihar Osun inda wata Baiwar Allah mai suna Toyin Adeniji tayi alkawarin dawo da bashin Gwamnatin domin a kara mata a nan gaba.

KU KARANTA: APC tayi wani bajimin kamu a Jihar Kano yayin da ake shirin 2019

Duk wanda ya cika sharudan da aka gindaya dai zai samu wasu karin kudi daga Gwamnatin Kasar domin ya karawa sana’ar sa karfi kamar yadda wani Jami’in Gwamnatin Tarayya ya fada.

Yemi Osinbajo ne ya shiga Jihar Osun da kan sa inda ya rabawa wasu ‘Yan kasuwa wannan kudi. Kamar yadda mu ka ji, wasu da aka rabawa wannan kudi a Karamar Hukumar Obokun sun yabawa Buhari.

Hakan na zuwa ne daidai lokacin da ake shirin zaben sabon Gwamna a Jihar Osun inda wasu ke ganin cewa Gwamnatin Buhari tayi amfani da wannan tsari ne domin cin ma burin ta na siyasa a kaikaice.

Dazu kun ji labari cewa wasu Magoya bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari sun maidawa wani Bawan Allah kudin sa da ya kashe wajen yakin neman zaben Muhammadu Buhari da Osinbajo a 2015.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel