Zaben Osun zai tabbatar da idan maganar Buhari gaskiya ne akan zabe mai inganci - Saraki

Zaben Osun zai tabbatar da idan maganar Buhari gaskiya ne akan zabe mai inganci - Saraki

Shugaban majalisar dattawa kuma dan takarar kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa karkasin jam’iyyar Democratic Party (PDP) , Bukola Saraki yace zaben gwamnan Osun zai nuna idan har da gaske shugaba Buhari zai jajirce kan zabe na gaskiya kamar yadda ya fadi.

Saraki ya bayyana hakan yayinda yake jawabi a lokacin da yake amsar matsayin da aka nada shi na shugaban kamfen din PDP a zaben gwamnan Osun.

Da yake Magana a Legacy House Abuja a ranar Litinin, 3 ga watan Satumba, Saraki wadda ya jagoranci kwamitin mutane 85 ya jadadda muhimmancin zaben ranar 22 ga watan Satumba, inda ya bayyana cewa shine zai zamo na farko tun bayan ziyarar Shugabar Jamus, Angela Merkal da Firai ministar Birtaniya Theresa May.

Zaben Osun zai tabbatar da idan maganar Buhari gaskiya ne akan zabe mai inganci - Saraki
Zaben Osun zai tabbatar da idan maganar Buhari gaskiya ne akan zabe mai inganci - Saraki
Asali: Depositphotos

KU KARANTA KUMA: Tazarcen Buhari zai kawo karshen duk shirmen nan na Saraki da Dogara – Yahaya Bello

Idan dai zaku tuna Shugaba Buhari ya jadadda cewa zai tabbatar da zabe na gaskiya . ya bayyana hakan a lokacin da Theresa May ta kawo ziyara kasar.

Ya kuma sake jadadda hakan a lokacin da yayi jawabi ga yan Najeriya dake zaune a kasar China.

Don haka Saraki yayi kira ga shugaban kasar da yayi kokari ya cika alkawarin da ya dauka.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel