Tazarcen Buhari zai kawo karshen duk shirmen nan na Saraki da Dogara – Yahaya Bello

Tazarcen Buhari zai kawo karshen duk shirmen nan na Saraki da Dogara – Yahaya Bello

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya bayyana zargin da ake yiwa Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara na kulla makirci na son wahaltar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin “shirme”.

An tattaro cewa abubuwa basa tafiya daidai tsakanin bangaren dokoki da na zantarwa a yanzu, wasu mabiya bayan shugaban kasa na zargin shugabannin majalisar dokoki da kin dawowa zamanmajalisa saboda su kawo tsaiko a ci gaban gwamnati mai ci.

Da yake jawabi ga magoya bayansa a gidansa dake GRA,Okene, Kogi, Bello yac Shugaban kasar zai yi nasara a tazarcensa sannan zai kawo karshen wannan shirmen da Saraki da Dogara ke yi.

Tazarcen Buhari zai kawo karshen duk shirmen nan na Saraki da Dogara – Yahaya Bello
Tazarcen Buhari zai kawo karshen duk shirmen nan na Saraki da Dogara – Yahaya Bello
Asali: UGC

Gwamnan wanda yayi Magana a harshen Ebira, yayi rokon cewa a zabi mambobin jam’iyyar a zabe mai zuwa.

Bello yace shine mutun na farko da Buhari ke nema alokacin da yake da wani lamari da yake son tattaunawa, cewaakwai alakar ‘da da mahaifi a tsakaninsu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: David Mark ya alanta niyyar takara kujeran shugaban kasa a 2019

A cewarsa, idan shugaban kasar na bukatar Magana da gwamna, “idan bai kira shi, toh babu wani mutun da zai iya kira.”

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel