INEC ta yi wa mutane sama da 50000 sabon rajistan zabe a Kaduna

INEC ta yi wa mutane sama da 50000 sabon rajistan zabe a Kaduna

Labari ya kai gare mu cewa Hukumar zabe na kasa watau INEC ta yi wa sababbin mutane sama da 500, 000 rajistar zabe a Jihar Kaduna. Sai dai da-dama ba su karbi katin na su ba har yau.

INEC ta yi wa mutane sama da 50000 sabon rajistan zabe a Kaduna
Shugaban Hukumar zabe na kasa Mahmud Yakubu a Majalisa
Asali: Depositphotos

Jaridar Punch ta rahoto cewa yayin da ake fara shirin zaben 2019, mutane 537, 874 ne INEC ta yi wa sabon rajista a Jihar Kaduna. A karshen watan nan da ya wuce ne Hukumar zaben ta tsaida rajistar masu kada kuri’a fadin Najeriya.

Malam Abdullahi Kaugama wanda shi ne babban Jami’in Hukumar zabe na Jihar Kaduna ya bayyana cewa cikin wadanda aka yi wa sabon rajistar, akwai mata 235,532. Sai dai kusan mutane 270, 000 ba su karbi katin zaben na su ba.

Maza fiye da 300, 000 ne aka yi wa sabon rajista a Jihar ta Kaduna.An samu wadanda aka gyara wasu kura-kurai a katin zaben su har mutum 29, 179. Bayan nan kuma akwai mutane fiye da 4,000 wadanda su ka samu matsalar hoto.

KU KARANTA: Jam'iyyar APC mai mulki za ta kori wasu 'Yan takaran ta

Za a cigaba da karbar katin zaben na PVC a Kananun Hukumomi har zuwa lokacin da za a fara shirin gudanar da zabe inji Abdullahi Kaugama. Babban Jami’in na INEC ya bayyana wannan ne wajen wani taro da Hukumar ta shirya a Jihar.

Wasu kuma dai an sake masu wajen zabe yayin da har yanzu akwai katin mutane fiye da 9000 da ba a gama bugawa ba. Babban Jami’in na IEC ya kuma yi alkawarin Hukumar ta INEC na kasa za tayi zabe na gaskiya da adalci a shekarar 2019.

Jiya kun ji cewa manyan ‘Yan takaran PDP sun hadu a Garin Kaduna. Masu neman takaran Shugaban kasar nan irin su Atiku Abubakar, Sule Lamido, Ibrahim Shekarau, Kwankwaso sun hadu ne wajen daurin auren yaron Ahmad Makarfi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel