Siyasar Kano: Yadda wasu Bayin Allah su ka shafa a keke domin ganin Takai

Siyasar Kano: Yadda wasu Bayin Allah su ka shafa a keke domin ganin Takai

Labari ya zo mana cewa wasu masu Matasa sun tuka keke tun daga Kauyen su domin haduwa da 'Dan takarar Gwamnan Kano na zaben 2019 a karkashin Jam’iyyar PDP watau Malam Sagir Salihu Takai.

Siyasar Kano: Yadda wasu Bayin Allah su ka shafa a keke domin ganin Takai
Wasu Bayin Allah daga Kauyen Katacho sun hadu da Takai a keke
Asali: Depositphotos

Saboda tsananin kauna, wadannan Bayin Allah sun tuko keke tun daga Garin Kachako da ke cikin Karamar hukumar Takai domin ganin Gwarzon su ‘Dan takarar Gwamna a Jihar Kano a zaben 2019 Sagir Salihu Takai.

Nazifi Nagge Kachako wanda shi ne Jagoran wadannan Samari da su kayi tafiya taka-nas domin nuna goyon-bayan su ga Sagir Salihu Takai ya bayyana cewa za su koma gidajen su ne a Kauyen Katchako a ken kekunan su.

KU KARANTA: Wani dakin ibada ya rufta da masu bautar Allah a Najeriya

Da su ke zantawa da manema labarai, wadannan Masoya na Malam Sagir Takai, sun bayyana cewa za su cigaba da yin irin wannan doguwar tafiya a kowace Ranar Juma’a har sai lokacin da PDP ta ba Takai tikitin takarar Gwamna.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Shugaban Kwamitin yakin neman zaben Salihu Takai a kafafen sadarwa na zamani Muhammad Bashir Amin, Garin Kachako dai yana da matukar nisan gaske zuwa ainihin cikin Birnin Kano.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel