Kowa a gidan mu zai zabi Shugaba Buhari a 2019 – Inji Bashir Ahmaad

Kowa a gidan mu zai zabi Shugaba Buhari a 2019 – Inji Bashir Ahmaad

Mun samu labari cewa wani Mai-ba Shugaban Shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara ya bayyana cewa Jam’iyyar APC za ta samu kuri’a sama da miliyan 2 a zaben Shugaban kasa na 2019.

Kowa a gidan mu zai zabi Shugaba Buhari a 2019 – Inji Bashir Ahmaad
Mai ba Shugaban kasa shawara yace Buhari zai ci Kano
Asali: UGC

Bashir Ahmad wanda shi ne ke ba Shugaban kasa Buhari shawara a kan kafofin sadarwa na zamani ya bayyana cewa APC ce za ta lashe zaben 2019. Ahmad yake cewa yana sa rai Buhari ya samu kuri’a 400 a gundumar sa.

Mai ba Shugaban kasar shawara ya kuma nuna cewa Buhari zai tashi da akalla kuri’u 200, 000 a Karamar Hukumar sa. Malam Ahmad ya fito ne daga Karamar Hukumar Gaya ko da dai yana zama a cikin tsakiyar Jihar Kano.

KU KARANTA: Shugabannin Majalisar da aka taba tsigewa a tarihin Najeriya

A bayanin da Bashir Ahmad yayi a shafin sa na Tuwita yace kowa a gidan su zai zabi Shugaba Buhari ne. Ahmad yace idan Allah ya so Shugaba Buhari zai samu kuri’a fiye da miliyan 2. 5 a zaben da za ayi na Shugaban kasa.

A zaben 2015 dai Shugaban kasa Buhari ya samu kuri’a kusan miliyan 2 ne a zaben Shugaban kasa. Gwamnan Jihar Kano na yanzu Abdullahi Umar Ganduje yayi alkawain cewa APC za ta samu kuri’u miliyan 5 a zabe mai zuwa.

Jiya kun ji cewa daya daga cikin ‘Yan takarar Jam’yyar PDP Sule Lamido yana cigaba da kai ziyara zuwa Jihohin kasar nan domin ganin ya samu goyon baya a zaben fitar da gwani na Jam’iyyar PDP da za ayi kwanan nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel