Labari cikin hotuna: Haduwar Buhari da Angela Merkel shugaban kasar Jamus a Villa
A ranar juma’a 31 ga watan Agusta ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakoncin shugaban kasar jamus, Angela Merkel a fadar gwamnatin Najeriya dake babban birnin tarayya Abuja, Aso Rock Villa.
Legit.ng ta ruwaito shugaban Jamus, Merkel ta isa Villa ne da misaln karfe 10:02 a safiyar Juma’a, inda Buhari ya tarbe ta a gaban fadar tasa, sa’annan ya gabatar mata da wasu ministocinsa, da manyan mukarrabansa suka gaisa.
KU KARANTA: Duniya ba matabbata ba: Alhazawan Najeriya 3 sun mutu akan hanyar Madina zuwa Makkah

Asali: Facebook
Kammala gaisawar tasu keda wuya, sai shugaba Buhari ya takwarar tasa suka sanya labule don tattauna batutuwan da suka shafi kasashen biyu
Wannan shine zuwan Merkel Najeriya na farko, kafin ta zo Najeriya sai da ta fara tsayawa a kasashen Ghana da Senegala, ziyarar da tace ta gudanar da shi ne don samun kyakkyawar alaka tsakaninta da kasashen duka.

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng