Masana'anta ita ce mabuɗin haɓakar tattalin arziki - Halima Dangote

Masana'anta ita ce mabuɗin haɓakar tattalin arziki - Halima Dangote

Babbar darakta ta kamfanin Dangote, Halima Aliko Dangote, ta nemi matasa dake fadin Najeriya da kuma nahiyyar Afirka akan su tashi tsaye wajen cudanya da gwagwarmaya a masana'antu da harkokin kasuwanci domin haɓakar tattalin arziki.

'Diya ga hamshakin attajiran nan kuma fitaccen dan Kasuwa, Alhaji Aliko Dangote, ta nemi mikewar matasa wajen jajircewa da kuma rike kasuwanci musamman harkokin noma domin haɓaka tattalin arziki da kawo ci gaban kasa.

Halima ta bayyana cewa wannan ita kadai hanya mafificiya kuma mabuɗi ga haɓakar tattalin arziki da kawo ci gaban kasa.

Masana'anta ita ce mabuɗin haɓakar tattalin arziki - Halima Dangote
Masana'anta ita ce mabuɗin haɓakar tattalin arziki - Halima Dangote
Asali: Depositphotos

Take cewa, lamari na tattalin arziki a duniya baki daya ya yi nuni da cewa jajircewar matasa musamman kan harkokin kasuwanci da noma ita kadai ce mabuɗin haɓakar tattalin arziki da za ta kai kowace al'umma kan tudun tsira.

KARANTA KUMA: Zaɓen APC a 2019 zai kara raba Najeriya - Lamido

Halima ta bayyana hakan ne yayin halartar taron kungiyar lauyoyin Najeriya karo na 58 da aka gudanar cikin babban birnin kasar nan na tarayya, inda ta ce kasashen Afirka har yanzu sun kasance cikin duhu ta fuskar tattalin arziki.

Ta kara da cewa, kididdiga ta bayyana cewa zuwa shekarar 2025, kaso 75 cikin 100 na ma'aikatan duniya za su kasance matasa wanda nauyin habakar tattalin arziki zai rataya a wuyan su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel