Fada a bainar jama'a: Yadda wasu mata 'yan Najeriya suka saida hali a kasar Indiya (Bidiyo)

Fada a bainar jama'a: Yadda wasu mata 'yan Najeriya suka saida hali a kasar Indiya (Bidiyo)

- Wasu 'yan mata daga Najeriya sun kunyata kan su a kasar Indiya

- Yan matan dai sun gwabza fada ne a bainar jama'a

- Wani dan Najeriya ne ya tona masu asiri

Sabanin yadda aka san mutanen kasar Najeriya da hazaka da kokari a duk inda suka samu kan su a fadin duniyar nan, wasu kuma suna ta kokari ne suga sun bata mana suna a idon duniya ta kowane fanni.

Fada a bainar jama'a: Yadda wasu mata 'yan Najeriya suka saida hali a kasar Indiya (Bidiyo)
Fada a bainar jama'a: Yadda wasu mata 'yan Najeriya suka saida hali a kasar Indiya (Bidiyo)
Asali: Facebook

KU KARANTA: Jirage 13 sun iso Najeriya makare da kayayyaki

Wani labarin takaici da ban haushi da muka samu shine na wasu 'yan mata daga Najeriya da suke zaune a garin New Delhi na kasar Indiya da suka zabi su saida hali a bainar jama'ar kasar.

Legit.ng ta samu cewa wani ma'abocin anfani da kafar sadarwar zamani ne mai suna Godson Osas ya watsa wani faifan bidiyo dake dauke da 'yan matan suna ta gabza fada ma kunya ba tsoron Allah a bainar jama'a.

Mista Godson Osas wanda ya bayyana takaicin sa a game da yadda matan suke neman batawa 'yan kasar suna, ya kuma yi Allah-wadai da irin shigar da suka yi ta banza wanda hakan ya sa ma mutane suka tsaya suna ta kallon su.

Haka zalika yayi Allah-wadai da yadda yace matan suna cin zarfin mutuncin sauran 'yan Najeriya wanda ya ce hakan na daga cikin dalilan da ya sa 'yan kasar Indiyan da jami'an tsaron su suka rena 'yan Najeriya.

Ba da dadewa ne ba dai sai bidiyon yayi ta yawo a kafafen sadarwar zamani inda 'yan Najeriyar da dama suka bayyana takaicin su game da 'yan matan tare da jan hankalin gwamnati da ofishin jakadancin kasar da su gaggauta daukar mataki a kan su.

Ga dai bidiyon fadan nan na 'yan matan:

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel