Tsohuwar Shugabar Majalisar Jihar Ogun ta tsere daga PDP

Tsohuwar Shugabar Majalisar Jihar Ogun ta tsere daga PDP

- Mrs Titilayo Oseni-Gomez ta sauya sheka daga PDP zuwa APC

- Tsohuwar ‘Yan siyasar tana neman kujerar Sanata a zaben 2019

- Oseni-Gomez ta taba rike Kakakin Majalisar dokokin Jihar Ogun

Mun samu labari cewa wata tsohuwar Kakakin Majalisar Jihar Ogun ta fice daga Jam’iyyar PDP inda ta koma Jam’iyyar ADC domin ta samu damar yin takarar Sanata a zabe mai zuwa na 2019 domin ganin ta taimakawa Yankin ta.

Titilayo Oseni-Gomez wanda fitacciyar ‘Yar siyasa ce a Jihar Ogun ta sauya sheka a kwanan nan inda ta kudirin niyyar tsayawa takarar kujerar Sanatat Ogun ta tsakiya a 2019 a karkashin sabuwar Jam’iyyar ta ADC da ta koma.

Rt. Hon. Oseni-Gomez ta bayyana wannan ne a gaban ‘yan jarida a Garin Abeokuta a jiya Alhamis. Oseni-Gomez ta farasiyasa ne tun a 1999 don haka ake ganin cewa za ta iya kawowa Jam’iyyar APC da kuma PDP cikas a 2019.

KU KARANTA: Saraki ya fadi dalilan da su ka sa yake neman tika Buhari da kasa

A 2013 ne Rt. Hon. Oseni-Gomez ta zama Kakakin Majalisar Jihar Ogun inda ta kafa tarihin zama macen farko da ta fara shugabantar Majalisar Jihar. Babbar ‘Yar siyasar tace ta yanke shawarar barin PDP ta koma Jam’iyyar ADC.

Manyan wadanda su ka tarbi tsohuwar ‘Yar Majalisar zuwa Jam’iyyar ADC sun hada da Nasir Isiaka wanda yana cikin masu neman Gwamnan Jihar a karkashin ADC da kuma jiga-jigan Jam’iyyar adawar irin su Joju Fadairo.

A Jihar Oyo dai ana ta hada kai tsakanin manyan Jam’iyyun adawa da kuma wadanda su ka balle daga APC domin a tika Jam’iyyar mai mulki da kasa a zaben 2019 a karkashin Jam’iyyar adawar ta ADC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel