Jami’an kwana kwana sun ceto wani mutumi yayin da gidan sama ya ruguzo a Kano

Jami’an kwana kwana sun ceto wani mutumi yayin da gidan sama ya ruguzo a Kano

Jami’an hukumar kwana kwana ta jhar Kano sun nuna bajinta yayin da suka ceto ran wani mutumi daga cikin baraguzan wani katafaren gidan sama daya ruguje a cikin birnin Kano, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin hukumar, Saidu Muhammad ne ya bayyana haka a ranar Alhamis 30 ga watan Agusta, inda yace da sanyin safiyar Alhamis ne ginin ya ruguzo, kuma ba tare da wata wata ba jami’an hukumar suka nufi inda abin ya faru, suka tarar da Muhammad Zakiru a cikin baraguzan ginin.

KU KARANTA: Rabonsu ya rantse: Gwamnatin jahar Kaduna na neman teloli don ta basu kwangila

“Da misalin karfe 6:45 na safe muka samu kira daga wani mutumi mai suna Musa Muhammad, dake zaune a unguwar kofar Na’isa, wanda ya bayyana mana cewar wani gida dake makwabtaka dashi ya ruguje.

“Samun wannan labari ke da wuya sai muka tattara jami’anmu, muka garzaya wurin da wannan ibtila’I ya faru da misalin karfe 7:20, anan muka tarar da ginin ya rutsa da Malam Mohammed Zakiri.

“Ba tare da bata lokaci ba tare da duba da halin da Zakiru ke ciki muka shiga aikin cetonsa gadan gadan, inda muka samu nasarar tsamoshi daga baraguzan gidan, sa’annan muka garzaya da shi zuwa asibitin Murtala don samun kulawa.” Inji Kaakaki Saidu.

Kaakakin hukumar kwana kwana ta jahar Kano ya kamma jawabinsa da yin gargadi tare da jan kunnen mazauna tsofaffin gidaje, da kuma ire iren gidajen da suka nuna alamar gajiywa ta hanyar tsatstsagewar bangonsu da su gaggauta tashi daga wadannan gidaje ko kuma su gyarasu, musamman a lokacin damuna don gudun rugujewa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel