Asiri ya tonu: Yadda aka cafke wasu yan luwadi turmi da tabarya a tsakiyar makabarta

Asiri ya tonu: Yadda aka cafke wasu yan luwadi turmi da tabarya a tsakiyar makabarta

Allah ya tona asirin wasu matasa yan luwadi a jihar Kano, yayin da aka kama suna turmi da tabarya suna aikata badala a cikin wata makabarta cikin birnin Kano, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Litinin data gabata na watan Agusta, inda wasu matasa a karamar hukumar Gwale suka kama yan luwadin a lokacin da suke tsaka da tafka wannan mummunan laifi.

KU KARANTA: Ku yi ma mayakan Boko Haram ruwan bala’I ba sassautawa – Babban kwamanda ga Sojoji

Wannan lamari yayi matukar bata ma mutannen wannan unguwa rai, inda suka fusata suka yi ma yan luwadin dukan kawo wuka, suka kusan kashesu, da kyar da sudin goshi Yansanda suka kwacesu.

Kaakakin rundunar Yansandan jahar Kano, Magaji Musa Majia ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace a yanzu haka matasan suna hannunsu, kuma bincike ya kankama zuwa yanzu.

Jama’a da dama a jihar Kano sun koka da karuwar matasa masu shiga mummunan dabi’ar nan ta luwadi inda namiji ke neman namiji, da madigo inda mace ke bin mace don samun biyan bukata, sai dai yawancin jama’an sun danganta lamarin ga illolin shaye shaye.

Sanannen abu ne luwadi babban zunubi ne a addinin musulunci, wanda yana daga cikin manyan laifukan da jama’an Annabi Lud suka tafka, wanda ya fusata Allah mai tsarki da daukaka ya saukar musu da azabarsa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel