NotTooYoungToRun: Jam’iyyar PDP za ta sawwakewa mata da matasa takara
Mun fahimci cewa Jam’iyyar PDP za ta sawakewa ‘Yan mata da kuma Matasa da ke shirin takara a karkashin Jam’iyyar adawar a zaben 2019.Hakan zai sa a samu karuwar matasa da mata a mulki.

Asali: Depositphotos
Kwanan nan ne babban Jam’iyyar adawar ta fitar da farashin fam din takara a zabe mai zuwa na 2019. Majalisar zartarwa na PDP ta yanke hukuncin rage farashin fam din takarar ‘Yan Majalisa domin ba matasa damar shiga takara.
Yanzu dai PDP ta rage kudin fam din tsayawa takarar kujerar Majalisar Tarayya daga Naira Miliyan 2 zuwa Naira Miliyan 1. Jam’iyyar ta dauki wannan mataki ne bayan an rage shekarun tsayawa takarar kujerar Majalisar Tarayya a kasar.
KU KARANTA: Wata sabuwar baraka na nema ta barke a Jam’iyyar PDP
Bayan haka kuma Jam’iyyar ta dauki matakin cewa mata ba za su biya ko sisi waje sayen fam din takarar kujerar Shugaban Kasa ko Gwamna ko kuma ‘Yan Majalisu ba. Hakan zai sa a samu mata sun shigo cikin lamarin siyasa a Najeriya.
Duk mai neman kujerar Shugaban kasa dai sai ya kashe Naira Miliyan 12 wajen yankan fam a karkashin Jam’iyyar PDP. Masu neman zama Gwamnoni kuma za su kashe Miliyan 6, yayin da masu neman takarar Sanata za su biya Naira Miliyan 3.5
Dazun ne Doyin Okupe yace Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ne kadai zai iya doke Shugaban kasa Muhammad Buhari a zaben 2019 domin mutanen Arewa ta tsakiya za su zabe sa a guje.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng