Girma ya fadi: Kotu ta daure wani Fasto shekaru 5 a Kurkuku kan satar kudi N984,450

Girma ya fadi: Kotu ta daure wani Fasto shekaru 5 a Kurkuku kan satar kudi N984,450

Wata kotun majistri dake zamanta a Igbesere na jihar Legas ta aika da wani Fasto zaman gidan yari na watanni hamsin da hudu bayan ta kamashi da laifin satar makudan kudade da suka kai N984, 450 daga bankin Wema, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Alkalin kotun A.T. Omoyele ce ta yanke ma Faston mai suna Olukayode hukuncin bayan ta kama shi da laifi, inda tace zai shafe watanni shidda a da shekaru biyu biyu akan duka tuhume tuhume uku da ake yi masa.

KU KARANTA: Magori wasa kanka da kanka: Na fi Buhari mutunci da kima a idon duniya – inji dan takarar shugaban kasa

Dansanda mai kara, Sajan Cyriacus Osuji ya bayyana ma Kotu cewa Faston ya aika wannan laifi ne a ranar 5 ga watan Maris na shekarar 2012, ta hanyar amfani da manhajar bankin na kan waya.

“Olukayode yayi amfani da wayarsa mai lamba 08034456771 ya saci kudi N22,550 daga bankin Wema, haka zalika Olukayode yayi amfani da wayarsa wajen aika kudi N701,900 daga bankin Wema zuwa bankin GTB, sai kuma ya kara aika N260,000 daga Wema zuwa asusunsa na bankin First Bank.” Inji shi.

Sai dai Dansandan ya tabbatar ma Kotu cewa bankin ta samu matsala daga ranar 4 ga watan Maris zuwa 4 ga wata na shekarar 2012, da wannan Faston wanda naira dari uku ne kawai a asusunsa yayi amfani da wannan dama ya saci kudaden.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel