Za mu yi irin abin da Hitler yayi a yakin Duniya a Akwa-Ibom a 2019 – Akpabio
Tsohon Gwamnan Jihar Akwa-Ibom watau Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa APC za ta karbe Jihar ta Akwa-Ibom a zabe mai zuwa na 2019. Kwanaki dai Akpabio ya sauya sheka zuwa APC.

Godswill Akpabio a karshen makon da ya wuce ya bayyana cewa za su karbe Akwa-Ibom daga hannun PDP a 2019 inda tsohon Gwamnan yace za su yi wa Jihar irin shigar da Adolf Hitler na kasar Jamus yayi wa Kasar Foland.
Sanata yace APC za ta dura Jihar Akwa-Ibom ne kamar yadda Sojojin Hitler su kayi wa Foland durar Mikiya a shekarar 1940 a lokacin yakin Duniya. A lokacin dai inji Sanatan, yaki ya ga Makiyan na Jamus kuma sun ga yaki.
KU KARANTA: An mani tayin kujerar Ekweremadu a baya - Abaribe
Akpabio wanda ya sauya sheka kwanan nan yace shi ba a daki ya zauna ya sanar da jama’a ta kafofin yada labarai na zamani cewa ya bar Jam’iyyar sa ba, sai dai tsohon Gwamnan ya koma Mazabar ne ya hada zugar gaske.
Wannan kalamai na tsohon Gwamnan bai yi wa jama’a dadi ba ganin yadda Sanatan ya kamanta zaben 2019 da kuma yakin Duniya. A lokacin yakin dai Dakarun Sojojin Jamus sun hallaka kusan kashi 20% na mutanen Kasar Foland.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng