Bikin Sallah: Jerin mutanen da su ka gana da Buhari a gidan sa na Daura

Bikin Sallah: Jerin mutanen da su ka gana da Buhari a gidan sa na Daura

A farkon makon nan ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zo Garin Daura domin yayi sallar idi. Hakan na zuwa ne jim kadan bayan Shugaban kasar ya dawo daga Landan inda yayi wani gajeren hutu.

Bikin Sallah: Jerin mutanen da su ka gana da Buhari a gidan sa na Daura
Shugaba Buhari tare da wasu Gwamnoni wajen bikin Sallah

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da Ministocin sa da wasu Gwamnonin Jam’iyyar APC na Najeriya. Daga cikin wadanda Shugaban kasar ya gana da su akwai wani daga Kudancin Najeriya wanda kwanan nan ya dawo Jam'iyyar APC:

1. Solomon Lalong

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da Gwamnan Jihar Fikato Salomon Lalong a gidan sa da ke Garin Daura a Jihar Katsina a jiya Laraba. Gwamnan sun sa labule ne da Shugaban kasar da rana tsaka.

2. Ibikunle Amosun

Kamar yadda mu ka samu labari daga fadar Shugaban kasar, Gwamna Ibikunle Amosun yana cikin wadanda su ka kawowa Shugaban kasa Buhari ziyrar sallah har gida. Gwamnan na APC ya hadu da Buhari ne bayan azahar.

KU KARANTA: Miyetti Allah na barazanar tsige Bukola Saraki

3. Orji Uzor Kalu

Shugaban kasa Buhari ya karbi bakuncin tsohon Gwamna Jihar Abia Orji Uzor Kalu wanda aka yi wa nadin sarauta a Garin Daura. Kalu ya nemi Inyamurai su daina yin nesa da Jam’iyyar APC mai mulki a kasar bayan ganawar.

4. Adebayor Shittu

Ministan sadarwan Najeriya Adebayor Shittu yana cikin wadanda su ka kai wa Buhari ziyara da bikin babban sallar nan. Shitu yace sun je gaida Shugaban kasar ne da yi masa ina gajiya bayan dawowar sa daga kasar Turai kwanaki.

5. Ayogu Eze

Shugaban kasa Buhari ya kuma gana da Sanata Ayogu Eze a gidan sa jiya. Hakan na zuwa ne bayan tsohon Sanatan na PDP ya sauya-sheka zuwa APC kwanan nan. Ana tunani Eze yana neman takara a Jihar Enugu a zabe mai zuwa.

Shugaban kasar ya gana da wasu daga cikin masu ba sa shawara a jiya Laraba da kuma ranar idi. Yau dai ake sa ran Shugaba Buhari ya dawo bakin aiki a babban Birnin Tarayya Abuja.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel