Aiyuka 4 da Buhari bai taba sanya mana baki ciki ba - Fashola

Aiyuka 4 da Buhari bai taba sanya mana baki ciki ba - Fashola

- Ministan Buhari ya bayyana yadda shugaban kasar yake sakar musu mara

- Shugaba Buhari kan tsame kansa daga cikin harkokin kwangiloli dare ya yarda iyalansa su saka baki

- Ministan ya kuma zayyana irin nasarorin da gwamnatin tasu ta samu

Ministan Aiyuka, gidaje da makamashi na kasa Babatunde Fashola ya bayyana muhimman aiyuka hudu da shugaban kasa Buhari ya ce dole ne ya yi su.

Aiyuka 4 da Buhari bai taba sanya mana baki ciki ba
Aiyuka 4 da Buhari bai taba sanya mana baki ciki ba

Babatunde Fashola ya bayyana cewa shekaru ukun da shugaban kasa Muhammad Buhari yayi akan karagar mulkin kasar nan, ya cimma wasu manyan aiyuka wanda yayi alkawarin yinsu.

Abin mamaki kan yadda aka gudanar da aikin shi ne yadda shugaba Buhari bai taba katsalandan ba wajen aiwatar da wadannan aiyukan

Ministan ya shaida cewa lamarin akwai mamaki ganin yadda shugaban kasar baya tsoma baki akan wanda za'a baiwa kwangilar.

KU KARANTA: EFCC ta bawa wani Sanata goron Sallah ta hanyar maka shi a kotu

Fashola ya kara da cewa shugaba Buhari bai taba turo wani zuwa ma'aikatarsa akan a bashi kwangila ko wata alfarma ta ba. Lamarin bai tsaya iya shugaban kasa ba, hatta matarsa bata tsoma mana baki akan yadda muke tafiyar da aikinmu.

Wanda hakan wani abu ne da ya zama bako a wannan lokacin, musamman idan aka yi al'akari da gwamnatocin da suka gabata.

Daga nan ne ministan ya bayyana manyan aiyukan da ma'aikatarsa ta bayar ba tare da samun umarni ko wani katsalandan ba.

1. Babbar Gadar Lagos wato second Niger Bridge

2. Babbar Hanyar Lagos zuwa Ibadan

3. Hanyar da ta tashi daga Ilorin zuwa Jebba ta Karasa zuwa Mokwa

4. Babbar Hanyar da ta tashi daga Abuja-Kaduna-Zaria zuwa Kano

Idan aka dawo harkar batun hasken lantarki kuwa, Fashola ya ce a cikin shekaru ukun da shugaba Buhari yayi, an samu nasarar samar da karin megawat 4,000 wanda adadin ya zama megawat 7,000.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel