Mutane 2 sun mutu a hatsarin mota a ranar Sallah

Mutane 2 sun mutu a hatsarin mota a ranar Sallah

Hukumar dake kula tsaron rayuka a hanya (FRSC) a jihar Ogun ta tabbatar da mutuwar mutane biyu a ranar Talata lokacin da wata motar kasuwa ta yi dungure a babban titin Lagas-Ibadan.

Kwamandan hukumar, Mista Clement Oladele ya fadama kamfanin dillancin labaran Najeriya cewa hatsarin ya afku ne da misalin karfe 5:00 na yamma a babban titin Lamona Park.

Mutane 2 sun mutu a hatsarin mota a ranar Sallah
Mutane 2 sun mutu a hatsarin mota a ranar Sallah

Ya bayyana ewa tayar motare ta fashe wanda yayi sanadiyar da motar ta dunga mirginawa.

KU KARANTA KUMA: Buhari da tsoffin shugabanni sun gazawa yan Najeriya – Dan takarar shugaban kasa

Mutane biyu ne suka rasa ransu a wannan hatsari yayinda wasu da dama suka jikkata, inda aka kwashe su zuwa asibitin Isara, Ogere.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel