Gwamnan jihar Enugu ya kai ma Musulmai ziyara a Masallaci ya nemi ayi ma Buhari addua

Gwamnan jihar Enugu ya kai ma Musulmai ziyara a Masallaci ya nemi ayi ma Buhari addua

Gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Uguanyi ya kai ma Musulmai ziyara a yayin da suke gabatar da Sallar Idi a babban masallacin jihar don taya su murnnar zagayowar ranar babbar Sallah, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Gwamna Uguanyi ya bukaci musulmai su yi amfani da wannan lokaci don yi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo addu’a.

KU KARANTA: Dakaraun Sojin Najeriya sun yi ma mayakan Boko Haram kisan kiyashi a wata arangama

Gwamnan jihar Enugu ya kai ma Musulmai ziyara a Masallaci ya nemi ayi ma Buhari addua
Gwamna

Uguwanyi ya smau kyakkyawar tarba daga al’ummar musulmai da suka halarci sallar, da suka hada da Sarkin Hausawan jihar Alhaji Abubakar Yusuf Sambo, kwamishinan Yansandan jihar, Danmallam Muhammad da shugaban hukumar DSS reshen jihar Enugu.

Gwamnan jihar Enugu ya kai ma Musulmai ziyara a Masallaci ya nemi ayi ma Buhari addua
Gwamna da Sarkin Hausawa

Haka zalika ya jinjina ma Musulman dake garin Enugu bisa zaman lafiyar da walwala dake jihar, wanda ya bayyana hakan ya kawo kariya ga rayuwa da dukiyoyin al’umman jihar, tare da samar da cigaba a jihar.

A nasa jawabin, Sarkin Sambo ya bayyana gamsuwar Musulman jihar da salon mulkin gwamnan, sa’annan ya yaba masa bisa sadaukarwar dayake nunawa wajen tafiyar da mulin jihar, daga karshe ya jaddada goyon bayan kafatanin Musulman jihar ga Gwamna Uguanyi.

Gwamnan jihar Enugu ya kai ma Musulmai ziyara a Masallaci ya nemi ayi ma Buhari addua
Gwamnan jihar Enugu

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: