Buhari yayi takawar mita 800, Obasanjo ya buga kwallon kafa, Jonathan ya motsa jiki - Yadda shugabannin Najeriya ke motsa jikinsu (hotuna)
Tun bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi tattaki na tsawon mita 800 daga masallain idi zuwa gidansa dake Daura a ranar babbanSallah, al’umman kasar ke ta tofa albarkatun bakunansu.
Wannan abu ya ba mutane da dama mamaki duba ga yawan shekarun shugaban kasar da kuma kallon da wasu ke yimasa na ganin bashi da cikakken lafiya.

Asali: UGC
Sai dai irin hakan ba akan shugaban kasar bane farau domin tsoffin shugabanin kasar da dama na da hanyoyi da irin sigar motsa jiki da suke yi.

Asali: UGC
Akwai lokacin da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya buga wasan kwallon kafa tare da jami’an gwamnatin jihar Ogun a lokacin bikin cikarsa shekaru 78 a duniya.

Abun mamaki sai gashi duk da tsufar sa, tsohon shugaban kasar ya yi nasarar jefa kwallaye biyu a raga.

Haka zalika tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba’a bar shi a baya ba wajen motsa jiki inda yake launin motsa jiki mai suna Jogging a turane.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Fusatattun matasa sun cinna wa kotun majistare wuta a Imo

Dukkanin shugabannin sukan jajirce wajen motsa jiki ne domin su karawa kansu kuzari da kuma gujema cututtukan zamanin musamman ma dai na bugun zuciya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng