Ba zan sanya baki a zaben fid da gwani na gwamna ba – Gwamna Shettima

Ba zan sanya baki a zaben fid da gwani na gwamna ba – Gwamna Shettima

Gwamna Kashim Shettima na jihar Borno ya yi godiya ga mutanen jihar akan irin biyayya da goyon baya da suka basa cikin shekaru bakwai da suka gabata.

Gwamnan yayi alkawarin cewa ba zai sanya baki a zaben fid da gwani wanda jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zata gabatar a jihar domin zabar dantakararta na gwamna ba.

A cewarsa Allah ne ke bayar da mulki ga wanda ya so.

Ba zan sanya baki a zaben fid da gwani na gwamna ba – Gwamna Shettima
Ba zan sanya baki a zaben fid da gwani na gwamna ba – Gwamna Shettima

Gwamnan ya kuma gargadi wasu yan siyasa wanda yayi zargin cewa suna satar arzikin kasar sannan kuma suka koma jam’iyya mai mulki domin son maye gurbinsa a 2019.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Fusatattun matasa sun cinna wa kotun majistare wuta a Imo

A baya Legit.ng ta rahoto cewa fadar shugaban kasa ta mayar da martani ga ikirarin gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal na cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari baida isashen lafiyar da zai sake takara karo na biyu.

Sai dai, Malam Garba Shehu, babban hadimin shugaban kasa a kafafen yada labarai yace takawar da shugaban kasar yayi ya isa martani ga Tambuwal.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel