Oshiomhole ya gana da shugabannin Edo ta Arewa

Oshiomhole ya gana da shugabannin Edo ta Arewa

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Mista Adams Oshiomhole ya gana da mambobi da shugabanni daga yankin Edo ta Arewa domin bikin babban Sallah da kuma tattaunawa kan lamuran siyasa a yankin gabannin zaben fid da gwani da za’a gabatar domin zabar yan takarar jam’iyyar a jihar.

A lokacin wannan rahoto, tuni mutane biyar da ake bukata a kowani mazaba daga kananan hukumomi shida sun fara tururuwa a gdan Oshiomhole na Iyamho.

Oshiomhole ya gana da shugabannin Edo ta Arewa
Oshiomhole ya gana da shugabannin Edo ta Arewa

A halin da ake ciki, kungiyar matasan Esan, sun hargitsa wani taro da Gwamna Godwin Obaseki a Irrua, karamar hukumar Esan ta tsakiya dake mazabar Edo ta tsakiya, kan zargin cewa gwamnan na so ya tursasa kwamishinan kudi na yanzu ya zama dantakarar sanata na yankin, inda suka nuna adawarsu akan haka.

KU KARANTA KUMA: Kwankwaso yayi bikin babbar sallah a wajen yawon neman shugaban kasa

A baya Legit.ng ta rahoto cewa gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana babba dalilin da ya sanya al'ummar kasar na masu kishi ke muradin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zarce har bayan 2019.

Gwamnan yake cewa, shawarar da masu kishin kasar nan su yanke na goyon bayan shugaba Buhari har bayan 2019 ba wani abu face tsagwaran neman hakikanin jagoranci na gaskiya gami da adalci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel