Shugaban Majalisar Dattawa ya kai ziyara wajen Edwin Clark

Shugaban Majalisar Dattawa ya kai ziyara wajen Edwin Clark

Jama’a sun fara sa alamar tambaya game da shirin Bukola Saraki na yin takarar Shugaban kasa a zaben 2019 bayan an ga Shugaban Majalisar Dattawwan na Najeriya tare da Cif Edwin Clark.

Shugaban Majalisar Dattawa ya kai ziyara wajen Edwin Clark
Bukola Saraki ya kai wa Edwin Clark a gidan sa

Shugaban Majalisar Dattawa ya kai ziyara wajen wani Dattijo da ake ji da shi a Kudancin Kasar nan watau Edwin Clark. Edwin Clark ya fito ne daga Kudu maso Kudancin Najeriya kuma ya taba rike mukamin Minista a baya.

Bukola Saraki ta shafin sa na sada zumunta na zamani na Tuwita ya tabbatar da cewa ya samu lokaci ya gana da Cif Edwin Clark. Saraki ya bayyana cewa ya dauki tsohon Ministan sadarwar kasar na Najeriya a matsayin Uban sa.

KU KARANTA: Ana fama da matsaloli a cikin Jam’iyyar APC Inji wani babba a Majalisa

Cif Edwin Clark yana cikin wadanda aka fi jin su a lokacin Gwamnatin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan wanda su ka fito daga Jihar Bayelsa. Saraki dai ya bayyana cewa yana tunanin tsayawa takara a zabe mai zuwa na 2019.

Yanzu haka dai Shugaban Majalisar Dattawan yana Jihar Kwara inda yake hutun sallah tare da jama’ar sa. A cikin makon nan ne ma dai tsohon Gwamnan ya gana da mutanen Mazabar sa a Garin Ilorin domin jin koke-koken su.

Clark yana cikin wadanda su ke cikin Gwamnati a lokacin mulkin Janar Yakubu Gowon kuma babu mamaki Saraki yana neman kamun-kafa a wurin sa. Kwanaki kun ji cewa Bola Tinubu yace Bukola Saraki na neman kujerar Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel